Connect with us

SIYASA

DA DUMI-DUMINSA: 2019: Gwamna Abubakar Da Sanata Bala Sun Kafa Sabon Tarihi A Bauchi

Published

on

Tarihin jihar Bauchi ba zai mance da cewar Gwamna Muhammadu A. Abubakar shi ne gwamnan da tun lokacin da a ka fara mulkin dimukradiyya wanda ya kasancewar gwamnan da ya fara yin mulki wa’adi daya ba tare da zuwa zango na biyu ba, domin kuwa INEC ta sanar da cewar dan takarar gwamnan jihar Bauchi na jam’iyyar PDP, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, shi ne ya kayar da gwamnan jihar Bauchi Muhammad da ke kan kujerar yanzu.

Da ya ke sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi a tsakar daren jiya Litinin, Babban Baturen zaben gwamnan jihar Bauchi, Farfesa Kyari Muhammadu, wanda shi ne mataimakin shugaban jami’ar FUTY da ke Yola, ya sanar cewar dan takarar PDP ya samu kuri’u guda 515,113.

Kyari ya shaida cewar dukkanin kuri’un da aka yi wa rijistan zaben a jihar su ne, 2,416,843; ya ce an tantance kuri’un masu zabe miliyan 1,143,019; inda kuma a ka kada kuri’u 1,133,966. Ya ce, kuri’u masu kyau su ne 1,111,406. Farfesan ya kuma shaida cewar an soke kuri’u 22,560.

Ya sake shaida cewar jam’iyyar PDP ita ce ta samu rinjaye da kuri’u 515,113, a yayin da APC ta samu kuri’u 500,625 a matsayin wance ta zo na biyu; PRP ta samu 46,326; a yayin da kuma GPN ta samu kuri’u 2,304 kacal da sauran kananan jam’iyyu da su ka samu sauran kuri’un.

Da ya ke shekanta wanda ya ci nasara a zaben na 2019, ya ce, “a bisa cike dukkanin sharudan zabe, kana da samun kuri’u mafi rinjaye a kan sauran ’yan takarar, ni Farfesa Kyari Muhammad Ina shaida cewar dan takarar gwamnan jihar Bauchi na jam’iyyar PDP, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, shi ne ya lashe zaben gwamnan jihar Bauchi na 2019 da dukkanin cike ka’idojin cin zabe.”

Wakilinmu ya shaida ma na cewar, Farfesa Kyari ya kai ga sanar da wanda ya ci nasarar lashe kujerar gwamnan jihar ne da karfe na 11: 20 daren nan.

A gefe guda kuwa, jama’ar jihar Bauchi, musamman matasa, sun fara gudanar da gangamin murna bisa nasanar da Sanata Bala ya samu.

“Mu na godiya ga Allah da ya tabbatar ma na da abinda mu ka zaba. Mu na godiya da a ka yi hakan,” a cewar wani matashi cikin daren da mu ka gana da shi.
labarai

Share This

Share this post with your friends!