Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Ra’ayoyi Na Bai Daya A Tsakanin Sin Da Faransa Wajen Tafiyar Da Harkokin Duniya

Published

on

A shekarar 2016, an kammala gina hanya mai lamba daya da ta hada birnin Brazzaville, babban birnin kasar Congo da kuma Pointe Noire, cibiyar tattalin arzikin kasar, hanyar dai ta rage tsawon lokacin zirga-zirga a tsakanin biranen biyu daga sati guda zuwa awa shida. Kamfanin CSCEC na kasar Sin ne ya dauki nauyin gina hanyar, a yayin da kamfanin EGIS na kasar Faransa ke sanya ido a kan aikin. Bayan da aka kaddama da hanyar kuma, Sin da Faransa sun sake yin hadin gwiwa da juna, inda kasar Sin take kula da aikin gyara hanyar, kuma Faransa ke gudanar da harkokin hanyar.
Hanyar ta kasance wani kyakkyawan misali na hadin gwiwar da Sin da Faransa suka gudanar a cikin wata kasa ta daban. Kasancewarsu kasashen dake da kujerar dindindin a kwamitin sulhun MDD, kasashen biyu na da tushe da kuma makoma mai kyau ta fannin yin hadin gwiwa, kuma hakan ya danganta ga ra’ayoyi na bai daya, ko kusan daya da kasashen biyu suke samu ta fannoni da dama. Kuma manufar kiyaye kasancewar bangarori daban daban na daya daga cikin ra’ayoyin.

A yayin da yake ganawa da babban sakataren MDD Antonio Guterres a bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna cewa, a halin da ake ciki yanzu na fuskantar farfadowar ra’ayi na kashin kai, da na ba da kariyar cinikayya, wadanda ke lalata tsarin kasa da kasa, da tsarin gudanar da harkokin duniya, an fi bukatar ra’ayin kasancewar bangarori da dama, da kuma MDD mai karfi. MDD alama ce ta ra’ayin bangarori da dama.
A nasa bangaren ma, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, shi ma na ganin cewa, “Ra’ayin kasancewar bangarori da dama hanya ce mafi dacewa wajen tinkarar kalubalen da ake fuskanta a duniya.” kuma ta wannan hanya ne, za a iya tabbatar da zaman lafiya mai dorewa, da tsaron duniya. A ganinsa, MDD na daukar matsayin daidaito wajen kiyaye daidaituwar duniya.
A fannin tinkarar sauyin yanayi, kasar Faransa na daukar matsayin sa himma wajen inganta batun, kasar Sin ma na daukar matsayi mafi muhimmanci na nuna goyon baya kan batun. An taba nazarta cewa, bayan da kasar Amurka ta janye jiki daga yarjejeniyar Paris, idan har kasar Sin ma ta janye jiki ta yin la’akari da bunkasuwar tattalin arzikinta, to yarjejeniyar Paris za ta zama wata takardar banza.

A hakika dai, ba kawai kasar Sin ta dauki alkawari kan yarjejeniyar Paris ba, har ma tana kokarin cika alkawarinta kan yarjejeniyar. A shekarar 2017, kasar Sin ta zuba jari na dalar Amurka biliyan 126.6 a fannin makamashin na bola jari, wanda ya kai kashi 45 cikin dari bisa na duk duniya baki daya, a fannin makamashin kiyaye muhalli.
Bisa rahoton da hukumar IRENA ta bayar a farkon shekarar bana, an nuna cewa, kasar Sin tana kuma matsayin gaba a duniya, wajen kira da fitarwa, da kuma amfani da batir mai aiki da hasken rana, da na’urar samar da wutar lantarki ta karfin iska, da batir da kuma motar lantarki.
Dalilin da ya sa Sin da Faransa suka cimma daidaito kan batutuwan tafiyar da harkokin duniya da dama, shi ne suna bin ra’ayin kasancewar bangarori da dama, da daukar alhaki bisa wuyansu.
A matsayinsa na kasar da ta cin moriyar dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya, da kuma bada gudummawarta, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a raya shawarar “ziri daya da hanya daya” ga dukkan duniya, kuma har zuwa yanzu kasashe da kungiyoyin duniya fiye da 150 amsa kirar. Yayin da yake ziyara a kasar Sin karo na farko a bara, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya fara da ziyartar birnin Xi’an, birnin da ya kasance mafari na “ziri daya da hanya daya”, inda ya sanar da cewa, Faransa ta shiga aikin raya “ziri daya da hanya daya”, kana ya ce wannan mataki ne na samun moriyar juna a tsakanin bangarorin biyu.
Kamar yadda shugaba Macron ya bayyana a shafin twitter bayan da ya yi maraba da zuwan shugaba Xi Jinping, inda ya ce, ya yi farin ciki da zuwan shugaba Xi Jinping da uwargidansa, kuma ziyararsa za ta zurfafa dangantakar hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, kana ta nuna cewa, Faransa da kungiyar EU, da kuma kasar Sin na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ra’ayin kasancewar bangarori daban daban a duniya. (Masu fassarawa: Lubabatu Lei, Bilkisu Xin, Zainab Zhang, dukkansu ma’aikatan sashen Hausa na CRI)
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!