Connect with us

LABARAI

Yadda Shugaba Xi Jinping Na Sin Yake Sha’awar Al’adun Faransa

Published

on

Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, tarihi, da ilmin falsafa, da ilmin adabi, da ilmin fasaha na kasar Faransa sun jawo hankalina sosai. Ya furta sunayen mashahuran masana a fannin ilmin fasaha na kasar Faransa, kana ya sha yin amfani da kalmomi da jimloli da suka shafi al’adun kasar Faransa, hakan ya bayyana sha’awarsa kan al’adun Faransa.

Na farko

Masu ra’ayoyi na kasar Faransa da shugaba Xi Jinping ke so

“Yayin da nake karanta litattafan tarihin kasar Faransa musamman tarihin babban juyin juya hali na kasar, na yi tunani sosai kan manufofin ingantuwar zamantakewar al’umma da siyasa ta dan Adam. Yayin da nake karanta litattafan Baron de Monteskuieu, da Boltaire, da Jean-Jackues Rousseau da sauransu, tunanina ya karu kan rawar da tunani da ra’ayoyi ke takawa a fannin raya zamantakewar al’ummar dan Adam. “kamar yadda yake kunshe cikin jawabin shugaba Xi Jinping a gun taron cika shekaru 50 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Faransa.

Na biyu

Wasu shahararrun marubutan kasar Faransa da Xi Jinping yake so

“Littattafan wasu shahararrun marubutan kasar Faransa da na karanta kamarsu Michel Eykuem de Montaigne, Jean de la Fontaine, Molière, Stendhal, Honoré de Balzac, Bictor Hugo, Alexandre Dumas, George Sand, Gustabe Flaubert, Alexandre Dumas. fils, Henri René Albert Guy de Maupassant, Romain Rolland, ya sa na kara fahimtar abubuwan da ke faruwa a zaman rayuwar dan Adam.”

–Jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi a ranar 27 ga watan Maris na shekarar 2014 yayin bikin cika shekaru 50 bayan kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Faransa.

Na uku

Masu fasaha ‘yan kasar Faransa da shugaba Xi Jinping ya ambata

“Jin dadin kallon abubuwan fasaha da Jean-François Millet, Édouard Manet, Edgar Degas, Paul Cézanne, Claude Monet, da Auguste Rodin, da kuma zane-zanen da Zhao Wuji suka zana bisa salon kasar Sin da na kasashen yammacin duniya, ya taimaka min wajen kara fahimtar harkokin da suka shafi fasaha.” —-A cewar Xi Jinping, a yayin babban taron tunawa da cikon shekaru 50 da kulla huldar jakadanci a tsakanin kasashen Sin da Faransa a ranar 27 ga watan Maris na shekarar 2014.

Na hudu

“The Red and The Black”da Stendhal ya rubuta ya yi babban tasiri, amma littattafan da Honoré·de Balzac da Guy de Maupassant suka rubuta sun fi sifanta yadda ake rayuwa a duniya. Alal misali, “The Human Comedy” da Balzac ya rubuta yana da tasiri sosai. Amma littattafan da suka fi burge ni su ne “Les Miserables” da “Kuatre-Bingt-Treize” da Bictor Hugo ya rubuta, wadanda ke da nasaba da lokacin juyin juya hali na Faransa. Yayin da nake karanta Bienbenu ya lallashi Jean Baljean a cikin littafin “Les Miserables”, hakika zuciyata ta girgiza sosai. Babu shakka, littattafan adabi na gari na iya girgiza koya wa mutane sosai. Ban da wannan kuma, ina sha’awar littafin “Jean-Christophe” da Romain Rolland ya rubuta.

—-jawabin da Shugaba Xi Jinping ya yi a taron tattaunawa kan aikin adabi da fasaha. (Ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 2014)

Na biyar

Karin maganar kasar Faransa da shugaba Xi Jinping ya taba amfani cikin jawabansa

Shugaba Xi Jinping ya sha yin amfani da karin magana na kasar Faransa a jawaban da ya gabatar, lamarin da ya shaida yadda ya fahimci al’adun kasar ta Faransa.

“Akwai nau’o’in karfi biyu a duniya, wato takobi da kuma tunani. Sai dai idan an yi hange na basira, tunani ya kan yi nasara a kan takobi.” (Napoléon Bonaparte), in ji shugaba Xi Jinping a jawabin da ya gabatar a hedkwatar UNESCO.

Kasar Sin tamkar zaki ne da ke barci, wanda idan ya farka, ko duniya ma za ta kadu. (Napoléon Bonaparte), in ji shugaba Xi Jinping a jawabinsa a yayin taron cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Faransa.

“Niyya kan haifar da hikima.” (Victor Hugo), in ji shugaba Xi Jinping a bikin bude taron sauyin yanayin duniya na birnin Paris.

“Sannu a hankali tsuntsu ya kai ga gina shekarsa.” (Karin maganar Faransa) in ji shugaba Xi Jinping a jawabinsa a yayin taron cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Faransa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!