Connect with us

RA'AYINMU

Matasa Da Sha’anin Zaben 2019

Published

on

Kafin zaben da aka gudanar a wannan shekara ta 2019, an yi zabubbuka a Nijeriya har sau biyar bayan dawowar demokradiyya, ma’ana, an yi a 1999, 2003, 2007, 2011 da kuma 2015.
ko shakka babu, a cikin wadannan zabubbuka guda biyar da aka aiwatar an samu koma baya ta fuskar matasa musamman a bangaren tsayawa takara ko neman mukaman siyasa. Hakan ya faru ne ba tare da la’akari da muhimmanci ko irin rawar da matasan ke takawa a lokutan zaben ba.
Har ila yau, an yi nasarar samun wadannan canje-canje ne a wannan shekara ta 2019, sakamakon dokar da Shugaban Kasa ya sanya wa hannu ta baiwa matasa damar neman kowane irin mukami a Nijeriya. Babu shakka, wannan ya baiwa dimbin matasa damar yanke shawarar tsayawa takarkaru domin neman mukamai iri daban-daban a kakar wannan zabe.
Kafin a kai ga sanyawa wannan doka da Shugaban kasa ya bijiro da ita hannu, idan muka dubi kundin tsarin mulkin 1999 na kasa, ya bayyana adadin shekarun wadanda suka cancanci tsayawa takara a matakai daban-daban na mulkin Siyasa. Takarar Shugaban kasa ya fara ne daga shekaru 40, Sanata 35, Majalisar tarayya 30, Majalisar jiha ita ma shekaru 30. A nan idan aka lura, za a gane cewa duk da irin mafi yawan gudunmawar da matasa ke bayarwa a harkokin zabe amma su ne mafi koma baya ta fuskar samun mukamai.
Haka zalika, mu a namu ra’ayin, baiwa matasa maza da mata dama a harkokin mulki, zai ba da damar bijiro da sabbin abubuwan ci gaba da kuma sauya al’amuran mulki baki daya. Kamar yadda Shugaban kasa ya rattaba wa dokar hannu, an rage shekarun takarar Shugaban kasa daga 40 zuwa 35, Majalisar tarayya da na jiha daga shekara 30 zuwa 25. Haka nan, Gwamna da Sanatoci su kuma aka bar su a shekaru 35, ba kamar yadda al’ummar Nijeriya suka nema ba. Rage yawan wadannan shekaru da aka yi, shi ne musabbabin da yasa matasa suka mike tsaye domin neman mukamai daban-daban a fadin wannan kasa.
Kazalika, rahotanni sun bayyana cewa, ba a taba samun yawan ‘yan takara a Nijeriya ba kamar a wannan zaben na 2019, don kuwa jam’iyyu 91 ne suka yi rajista, masu neman Shugabancin kasa 73, masu neman kujerar Sanata 1,904, masu neman kujerar Majalisar tarayya 4,680, masu neman kujerar Gwamna, 1,066, da kuma masu neman kujerar Majalisar Jiha su kimanin 14,583.
A zahiri, wannan zabe ya nuna irin bajinta tare da yunkurin da matasa suka yi don ganin su ma an dama da su a wannan lokaci. Haka nan, a dai wannan lokaci matasa sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin sun mallaki rajistar zabe tare da tsayawa takarkaru na gurabe daban-daban.
Haka zalika, manya-manyan bangarorin da aka fi mayar da hankali a kansu a wannan zabe na 2019 su ne, yadda matasa suka yi yunkurin neman kujerar ‘Yan Majalisa, Shugaban kasa, Gwamna da kuma Sanatoci. Wannan kuwa ya faru ne sakamakon rage yawan shekaru da aka yi don su ma matasan su samu damar shiga su taka tasu rawar. Kaso 10 zuwa 14 na wadanda suka tsaya takarar Shugaban kasa matasa ne.
Haka nan wadanda aka tsayar a matsayin Mataimakan Shugaban kasa mafiya yawan su ba su wuce shekaru 35 zuwa 40 ba. Kazalika, an samu karin yawaitar matasa da suka tsaya takarar Majalisar tarayya a 2015 daga kaso 18 zuwa 27.4 da suka nemi takara a jihohi 29 matasa ne, inda kusan kaso 22.9 kuma aka tsayar da su a matsayin kujerar Mataimakin gwamna.
A karshe muna sake jan hankali tare da nuni cewa, ko shakka babu adon demokradiyya da dorewar ta na da alaka kai tsaye da baiwa kowane bangare na kasa da sauran al’umma damar taka rawa a kowane gurbi ko mukami musamman a bangaren matasan da suke su ne kashin bayan al’umma da kuma tafiyar da ita kanta demokradiyyar a ko’ina a duniya.
Haka zalika, wannan gidan Jarida na da buri ko bukatar ganin kowace Jam’iyya ta ci gaba da gudanar da al’amuranta kamar yadda dokokin Jam’iyyar suka tanadar mata, ma’ana, a tabbatar an ci gaba da tafiyar da ita bisa dokokin da aka kafa ta. Ko shakka babu wannan zai taimaka wajen dorewar demokradiyya tare da baiwa Matasa damar ba da tasu gudunmawar a kowane mataki da bangare na wannan kasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!