Connect with us

SIYASA

Zaben Jihar Kano: PDP Bata Da Gamsasshiyar Hujja Kan Korafin Da Take Yi – Kwamishina Muhammad Garba

Published

on

Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai, Matasa da wasanni na Jihar Kano Malam Muhammad Garba ya bayyana cewa kamata ya yi dan Takarar Jam’iyyar PDP a Jihar Kano ya karbi kayen da ya sha da kyakkyawar niyya ya amince cewa wannan shi ne zabin al’ummar Kano da suka yiwa Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Wannan bayani na cikin jawabin da Kwamishinan Ma’aikatar yada Labaran na Jihar Kano Malam Muhammad Garba ya gabatar na matsayin martani kan tattaunawar da Abba Kabir Yusif ya yi da Jaridar Daily trust ta ranar Lahadi, inda yake kalubalantar sakamakon zaben da ya gudanar karo na biyu a Jihar Kano wanda ya sake tabbatar da Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, hakan ke tabbatar da faduwar da dan takarar gwamnan Jam’iyyar ta PDP wanda har yanzu ke masa yawo a zuciya.
Malam Muhammad Garba ya kara da cewa Jam’iyyar PDP da dan takarar ta sun gaza samar da tabbatacciyar hujja da zasu kalubalanci zaben da akayi ittifaki shi ne mafi sahihanci, ya ci gaba da cewa yunkurin da suke ta hanyar munanan kalamai domin harzuka jama’a alokacin zabe da kuma bayan kammala zabenduk ya kasa yin wani tasiri, yanzu kuma sun ci gaba da nuna cewa Jam’iyyar APC ce tayi sanadiyyar rashin nasararsu. Kwamishinan Ma’aikatar yada Labaran na Jihar Kano ya ci gaba da cewa tun daga kan sakamakon zaben Gwamna na ranar 9 maris ya nuna yadda aka samu Jam’iyyar PDP da hannu cikin aringizon kuri’a da kuma yadda wakilanta ke dangwalen kuri’u wanda daga baya aka gano haka kuma Hukumar zabe mai zaman kanta ta bada umarnin tafiya zabe zagaye na biyu a wasu akwatunan zabe a kananan Hukumomi 28 na Jihar Kano.
Muna da cikakkun bayanai da shedun yadda wakilansu suka yi aringizon kuri’a, sayen katin zabe, dangwale, tayar da hankalun al’umma da cin zarafin masu zabe. A kwai ma wasu wuraren da matukar kana son yin zaben sai dai ka amince da zabar Jam’iyyar PDP. Ya ci gaba da cewa fadar da suke wai zaben zagaye na biyu cike da yake da rikici da kuma kashe kashen jama’ar da basu jiba kuma basu gani ba, har yanzu babu wata hujja dake tabbatar da wannan zargi, ba wata takarda ko wata shaida da ke tabbatar da wannan zargi wanda ‘yan barandar su dake amfani da kafafen sadarwa na zamani keta yada ire iren wadanan labarai wanda suke amfani da wasu rikice rikicen kabilanci ko na addini da suka taba faruwa a wasu jihohin a tarayyar Najeriya da ma kasashen waje. Saboda haka sai Kwamishinan Ma’aikatar yada labarin na Jihar Kano Malam Muhammad Garba ya tabbatarwa da Jama’a cewa wannan zango na biyu na Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai kasance inganci da nasara sama da zangon farko domin dorawa ne kwai akan irin nasarorin da aka cimma akan na zangon farko, yace wannan nasara ke tabbatar da kyawawan ayyukan alhairi shekaru hudu da suka gabata.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!