Connect with us

SIYASA

Fintiri Ya Kafa Kwamitin Bincike Mai Mutum 67

Published

on

Zababben gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya kafa kwamitin mutum 67 domin bincike, tattara duk bayanai gwamnati, daga shekara hudu na tsohowar gwamnatin Umaru Bindow Jibrilla, zuwa sabowa.
Da yake rantsar da mambobin kwamitin ranar litinin a Yola gwamna Umaru Fintiri, ya kuma bukaci kwamitin da ta yi kyakkyawan bincike da kawo mishi rahoton gaskiya game da harkokin kudaden shigar da jihar ke samu.
Kwamitin mai mutum sittin da bakwai, wacce tsohon babban sakataren ma’aikatar gwamnatin tarayya Aliyu Sama’ila Numan ke jagoranta, ana tsammanin ta mika rahotonta kafin ranar 29/5/2019.
Gwamnanan ya ci gaba da cewa “Ku binciki cikakken bayanin harkokin kudaden da yake kasa da wanda akebin gwamnatin jiha.
“Ku binciko duk ayyukan da gwamnati mai barin gado ta bayar, ku kawo mana gaskiyar kudaden da’akabiya, da kudaden da’akebi akan duk wani aikin da’aka bayar.
“gwamnati na zata bada cikakkiyar kulawa ga kananan hukumomi, domin a samu ingantaccen ci gaba, don haka ku tantance kudaden shigar da kananan hukumomin ke samu da wanda suke samarwa, ku kawo rahotonku kafin ranar rantsar da sabowar gwamnati” inji Fintiri.
Da yake maida kalami shugaban kwamitin Alhaji Aliyu Isma’ila Numan, ya bada jama’ar jihar tabbacin kwamitin zaiyi aiki da kwarewa, domin samar da ingantacciyar tarwira mai ma’ana ga sabuwar gwamnati mai zuwa.
Numan, ya kuma baiwa zababben gwamnan tabbacin kwamitin ba zai ba marada kunya ku jawo suka ga gwamnatin ba.
To sai dai wannan na zuwa lokacin da rikici ya’yi zafi tsakanin manyan jiga-jigan jigogin siyasar jihar, kan batun raba mukaman gwamnati mai shigowa.
Bayanai dai na nuni da cewa bayan da sabon gwamna Umaru Fintiri, ya kammala raba manyan mukaman gwamnatinsa, sai kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar (bashi a kasar), ya ce ba haka za’ayi ba.
Bayanai sun tabbatar ma LEADERSHIP Ayau cewa “an tsara banbaren Aisha Buhari an basu kwamishinoni bakwai, bangaren tsohon gwamna Murtala Nyako an basu kwamishinoni biyar, PDP ta tashi da kwamishinoni gomasha daya.
“bayan an kammala an amince da haka Atiku yaji labari yana Dubai ya ce ba zai yiwu ba, kuma gwamnati tamkar hanun jari ne kowa da jarin da ya shigar” inji bayanan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!