Connect with us

SIYASA

Gwamnan Gombe Mai Jiran Gado Ya Kaddamar Da Kwamitin Amsar Mulki

Published

on

Zababben Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Inuwa Yahaya, ya kaddamar da kwamitin tabbatar da an samu mika ragamar mulki daga hannun gwamnati mai barin gado a ranar 29 dga watan Mayu 2019 cikin tsanaki ba tare da wani matsala ba.
Kwamitin ya samu shugabancin Alhaji Mohammed Kabiru, tsohon Darakta Janar na Hukumar Fansho ta kasa, yayin da Alhaji Zubairu Umar zai kasance a matsayin sakataren kwamitin.
A jiya Talata ne zababen gwamnan ya kaddamara da kwamitin a grain Gombe ya kuma kaddamar da wasu kwmaitoci 23 da za su lura da sauran al’amurran yadda za a gudanar da karbar ragamar muliki daga gwamnati mai barin gado cikin tsanaki ba tare da matsala ba.
A jawabinsa, Alhaji Inuwa Yahaya ya bayyana cewa, ana bukatar kwamitin ta samar da tsarin da za ayi amfani da shi wajen karbar harkokin mulki daga gwambati mai bari gado, tare kuma da tantance dukkan kaddarorin gwamnati dake ciki da wajen jihar nan gaba daya, da tabbatar da an gudanar da bikin mika mulki cikin tsanaki ba tare da wani matsala ba.
Haka kuma ana bukatar kwamitin ta tantance dukan bayanan da gwamnati mai barin gado ta bayar tare da kuma ba gwamnati mai jiran gado shawarwarin a suka kamata.
An kuma dora wa kwmaitin nauyin tantance dukkan kudaden gwamnati dake a bankunan kasar nan da kuma basusukan da ake bin ta.
Zababben gwamnan ya kuma bayyana cewa, kwamiti 23 da aka kuma kafa suna da aikin lura da ma’aikatu 27 da ake dasu, su kuma bayar da shawarwarin da suka kamata don samun cikakkiyar ci gaba.
Alhaji Yahaya ya kuma bayyana cewa, ana sa ran kwamitocin za su mika rahotainsu kafin ranar rantsar da sabuwar gwamnati, 29 ga watan Mayu, wato mako uku bayan raatsar da su.
Haka kuma ya ce, ba na kafa kwamitin don bincike da kawo wa wani matsala bane, an kafa ne don samn saukin tafiyar da karbar mulki, inji shi..
A martaninsa Shugaban kwamitin, Alhaji Kabir ya gode wa zababben gwamnan a bisa dora musu wannan aikin, ya kuma yi alkawarin yin aikin yadda ya kamata don ci gaba jihar.
Da yake tsokaci a yayin kaddamar da kwmaitocin, Alhaji Danjuma Goje, jagoran jam’iyyar APC a jjihar Gombe, ya ce an zabo ‘yan kwamitin ne saboda mutumcinsu da kuma kawarewarsu a harkokin gudanar da ci gaba al’umma, ya kuma bukaci wadanda basu samu shiga kwamitin ba da su kara hakuri don kuwa a kwai wasu aiki na nan zuwa nan gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!