Connect with us

SIYASA

Kotun Kararrakin Zabe Ta Amshi Korafe-korafe 26 Kan Zabe A Bauchi

Published

on

Kotun sauraron korafe-korafe kan zabe a jihar Bauchi ta shaida cewar kawo yanzu ta amshi korafe-korafe har guda ashirin da shida (26) da aka shigar a gabanta ana kalubantar zabe a kujeru daban-daban da suka kunshi majalisar tarayya da ta jihar da kuma zaben sanatoci.
LEADERSHIP Ayau ta nakalto cewar kotun tana da alhakin sauraron kararrakin da suka shafi zaben gwamnan jihar, sanatoci, majalisar tarayya da kuma majalisar jihar ta Bauchi.
Bello D. Abdullahi Sakataren Kotun amzar korafe-korafen zabe a Bauchi shine ya shaida wa manema labaru hakan a jiya, yana mai shaida cewar ya zuwa yammacin jiya da yake ganawa da ‘yan jaridan, sun amshi korafe-korafe har guda 26 da aka shigar a gabansu.
Ya ce, daga cikin wadannan kesa-kesa din, guda goma sha daya (11) sun kunshi majalisar dokoki ta jihar Bauchi; bakwai (7) sun kunshi kujerar sanatoci daga mazabu uku na sanatoci da ake da su a Bauchi, inda kuma ya kara da cewa kararraki guda takwas (8) sun amsa ne kan kujerar majalisar tarayya.
Bello ya kara da cewa dukkanin mazabun sanatoci guda uku sun amshi korafe-korafe a kansu, yana mai karawa da cewa har zuwa yanzu masu shigar da kara suna da zarafin shigar da kararrakinsu gabanin karewar lokacin da aka ware domin amsar korafe-korafen.
Sakataren kotun ya shaida cewar ya zuwa lokacin da yake ganawa da wakilinmu, ba su amshi korafi kan zaben gwamnan jihar Bauchi ba, “Har zuwa yanzu ba mu amshi kora kan zaben gwamna ba, amma ba zan ce babu ba don har yanzu kofa a bude take, don wani karar ba a tashi shigar da shi sai daf lokacin rufe amsar korafe-korafen, amma kawo yanzu babu wani karar da aka shigar kan zaben gwamnan jihar,” A cewar shi.
Ya kuma shaida cewar ba su kai ga sanya lokacin fara sauraron kararrakin ba, yana mai karawa da cewar a daidai wannan lokacin suna kan matakin amsar korafe-korafe daga wasu korafi akan zaben ne. ya kuma ce, dukkanin mai korafi yana da cikakken damar shigar da kara a gaban kotun.
Ya ce da zarar suka kammala dukkanin tsare-tsare za su fara sauraron kararrakin da suke gabansu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!