Connect with us

SIYASA

‘Yan Majalisun Tarayya Na Goyon Bayan Takarar Gbajabiamila, Inji Hon. Soro

Published

on

Zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Darazo/Ganjuwa da ke jihar Bauchi, Hon. Mansur Manu Soro ya shaida cewar mafi yawan ‘yan majalisun Tarayya suna goyon bayan Femi Abdulhakeem Gbajabiamila da ya zama sabon Kakakin Majalisar tarayya, a Majalisar da za a kaddamar ta 9.
Soro ya shaida hakan ne a hirar da ‘yan jarida a Bauchi, yana mai karawa da cewa, Hon. Gbjabiamila dan Majalisa ne da ya samu gogewa sosai da ilimin sanin harkokin majalisar, inda ya shaida cewar ya cancanci zama Kakakin Majalisar ta tarayya domin kyautata shugabanci da kyautata Nijeriya.
Manu Soro ya ce, suna masu goya wa Hon. Gbajabiamila ne a bisa kasancewa dan Majalisar da ya dace kuma mai cikakken biyaya wa jam’iyyar APC da ya ce zai kyautata shugabanci idan ya zama Kakakin Majalisar.
Manu ya ce za su tabbatar da mara ma wanda zai yin aiki tare da sashin zartarwa domin cimma muradin kyautata Nijeriya ba tare da kawo wa gwamnati tarnaki ba.
Ya ke cewa, “Femi Abdulhakeem shugaba ne da zai yi kokarin hada kan majalisa wuri guda da shawo kan matsalolin da suka addabi Nijeriya, ya na da kwarewar da zai fitar da tsare-tsaren da Nijeriya za ta mora sosai. Muddin muka zabeshi a majalisa ta Tara lallai za mu yi gayar farin ciki da kasancewarsa a matsayin shugaban majalisar wakilai ta tarayya,” A cewar shi.
Yana mai shaida cewar, zabbabbun ‘yan Majalisar da suke jiran rantsuwa suna sane da irin kura-kurai da majalisa ta 8 ta tafka musamman kan jan kafa wajen amincewa da aikace-aikacen gwamnatin tarayya wanda hakan ya kawo nakasu ga aiwatar da wasu aiyukan ci gaban kasa.
Ya ce, mambobin majalisar suna da muradin samun shugaban da zai tabbatar da yin aiki kafada-kafada da Majalisar zana doka da kuma ta zartaswa domin ci gaban kasa a kowani lokaci.
“Muna son mu tabbatar wa jama’an da suka zabe mu cewar mu a lokacinmu za mu tabbatar da amincewa da kasafin kudi akan lokaci, amincewa da kudirorin da suka zo daga gwamnatin tarayya wadanda za su kyautata rayuwar ‘yan Nijeriya wadanda don sune ma suka zabemu, a takaice za mu sanya muradin ‘yan kasa a matsayin muradin farko kafin zuwa ga wani abun,” A cewar shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!