Connect with us

SIYASA

Gwamna Gaduje Da Mataimakinsa Sun Karbi Shaidar Lashe Zabe

Published

on

A ranar Labara ba ne Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje Da Mataimakinsa Dakta Nasiru Yusif Gawuna da kuma sauran ‘yan majalisar dokokin Jihar Kano 40 suka karbi shaidar lashe zaben wanda aka gudanar akonnin biyu da suka gabata, Kwamishinan Hukumar Zabe mai kula da shiyyar Kano, Jigawa da Katsina Injiniya Abubakar Nahuce ne ya damka masu wannan takardar shaidar lashe zabe, Da yake gabatar da Jawabinsa Injiniyar Abubakar Nahuce ya yi tsokaci kan abinda ake ta cece ku ce akansa musamman Kalmar rashin kammalar zabe, wanda yace ya kamata jama’a su fahimci cewar duniya ta ci gaba wanda yanzu saboda cigaban da aka samu ba zai yiwu ace an ci zabe da rinjaye kalilan ba musamman a inda akwa samu soke kuri’un da suka haura tazarar dake tsakanin ‘yan takara. Saboda haka sai ya jinjinawa al’ummar Jigawa, Kano da Katsina bisa yadda zaben ya gudana.
Shima da ya ke gabatar da nasa Jawabin jim kadan da karbar takardar shaidar lashe zaben Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bayan godiyarsa ga Allah wanda ya bamu wannan nasarar lashe zaben da ya gudana, Ganduje ya bayyana cewa ya zam wajibi mu tabbatar da samar tsarin da inganta rayuwar matasanmu, yace dole mu tabbatar da iimin mata kyauta, haka kuma kamar yadda aka sani noma na cikin babbar sana’ar al’ummarmu don haka za muyi duk mai yiwa waje inganta harkar noma Gwamna Ganduje acikin jawabinsa ya kuma tabbatar da aniyar gwamnatinsa na hada karfi da masu zuba jari domin samar da tallafi ga matasanmu, yace aikin gina Kano ba na mutum guda bane shi kadai, aiki ne da yake bukatar shigowar kowa da kowa, yace ba za’a samu cigaban da ake bukata ba har sai jama’a sun zage damtse wajen hada karfi kan cigaban Jihar Kano Akarshe Gwamna Ganduje ya godewa Jama’ar Kano bisa sake amincewa da sahalle masa ci gaba da jagorantar Jihar a zango na biyu, yace da yardar Allah zamu tabbatar da ganin bamu baiwa al’ummar Kano kunya ba, zamu yi bakin kokari wajen tafiya da duk wanda ke bukatar kawowa Jihar nan tamu mai albarka cigaban da ake fata.
Taron ya gudana a dakin taro na Shelkwatar Hukumar zabe mai zaman Kanta, cikin wadanda suka halarci bikin karbar takardar shaidar lashe zabe akwai sanatocin Kano guda uku wanda suka hada da Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano Sanatan Kano ta tsakiya, Kabiru Ibrahim Gaya wakilin al’ummar Kano ta Kudu da Kuma Sanata Barau I Jibrin mai wakilta Kano ta Arewa. Haka kuma akwai ‘yan Majalisar Wakilai ta tarayya, majalisar dokokin Jihar Kano, Kwamishinoni, mashawarta na musamman da sauran dubun dubatar magoya baya ne suka dafawa Gwamna Ganduje da Gawuna zuwa karbar wannan takardar shaidar sake lashe zaben kujerar Gwamnan Kano.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!