Connect with us

RA'AYINMU

Ku Yi Maganin Wannan Yayin Da Ake Yi Na Kashe Kai

Published

on

Shekaru masu yawa da suka shige, babu wanda zai yi zaton wani dan Nijeriya zai iya yin tunanin kashe kansa, ko da kuwa a kan kowane irin dalili ne, ballantana ma a ce har ya kashe kan na shi din.
A wancan lokacin an san ‘yan Nijeriya da sanin daraja da kimar rayuwa. Amma a halin yanzun shedanin da ke cikin jikin dan adam ya fara bayyana a cikin al’ummar namu. Mawuyaci ne a wayi gari ko mako guda ya wuce ba tare da ka ji labarin wani ko ma wasu ‘yan Nijeriyan sun kashekansu ba. Kadan ne kadai daga cikin irin wannan abin asshan ake jin labarin aukuwan su a kafafen yada labarai, yakan faru a kuma yi watsi da shi tamkar dai ba wani babban abu ne ya auku ba.
Al’umman Duniya kanta, ta fara nuna damuwarta a kan yawaitan annobar kashe kai da yake faruwa a Nijeriya, kan hakan ne kididdiga ta bayyana kasar nan a matsayin ta biyar a duk Duniya na yawan mutanan da ke kashe kansu, wanda kuma hakan ke nuna tamkar ba wani abin damuwa ne ba a wajen hukumomin na Nijeriya, kama daga gwamnatin tarayya, gwamnatocin Jihohi da na ma na kananan hukumomi.
A ranar 29 ga watan Yuli, 2018, mujallar nan ta kididdiga wacce ake kira da,Spectator Inded, ta wallafa wani rahoto na hukumar lafiya ta Duniya (WHO), wanda ya yi kididdigan yawan mutanan da kan kashe kansu a cikin kowane jumla na mutane 100,000, a kowace kasa. Wannan rahoton ne ya lissafta Nijeriya a matsayin kasa ta Biyar, inda a rahoton ya nuna a kan sami mutane 15,000, da sukan kashe kansu a cikin kowane jumla na mutanen Duniya 100,000.
Qasar Koriya ta kudu ce a sahun gaba sai kasashen Rasha, Indiya da Japan da suke rufa mata baya.
Hakanan, manyan kasashen da suka ci gaba kamar, Amerika, Faransa, Austreliya da Canada har ma da Afrika ta kudu, duk sun bayyana a jerin kasashen da akan sami al’ummun su suna kashe kansu a bisa wasu dalili, sa’ilin da kasar Saudiyya, ta zama na 17 a jerin kasashen da al’ummun na su kan kashe kansu da mutane 3,900 a cikin duk mutanan kasar 100,000.

Masana cutukan kwakwalwa a Nijeriya suna alakanta kisan da wasu ‘yan Nijeriya ke yi wa kawukan su ne da talauci da shiga cikin wani yanayi na damuwa, a sabili da watsar da lamarin su da wadanda ya kamata su nuna damuwa a kansu suka yi, rashin tabbas, rashin aikin yi da kuma rasa wani abin kaunar su ko wata kadarar su.
Wasu dalilan kuma sun hada da, faruwan wasu muggan cutuka, wadanda a lokuta da yawa sukan haifar da yin ritaya daga baya kuma mutum ya kai ga kashe kansa.
Qididdiga ya nuna kashi 90 na mutanan da sukan kashe kansu suna fama ne da wani nau’i na cutukan kwakwale.
Yanzun da kuma baya, ‘Yan Nijeriya sukan yi yunkurinkashe kansu ne a sanadiyyar babewan wata soyayya, tsoro ko kuma faduwan wata jarabawa, rasa aikin da mutum ke yi ko kuma rasa wata sana’a da yake cin abinci daga gareta, tsabagen bashin da aka rasa yanda za a yi da shi, a wasu lokutan ma hatta tsangwama daga dangi kan haddasa hakan.
Akwai matukar damuwa a kan dimbin matsi da talaucin da ke addaban ‘yan Nijeriya a halin yanzun, wandaba zai yiwu a kawar da kai daga gare shi ba. matsalar rashin aikin yi yakan kai halin da matasanmu da suka kammala karatun su tare da kyakkyawan fata amma kuma a karshe hatta ‘yan kananan ayyukan da a bayaba sa tunanin su, su kasa samuwa a gare su.
Domin samun ci gaba da rayuwa a irin wannan mawuyacin halin, da yawan ‘yan Nijeriya, musamman matasa, sukan sami kwanciyar hankalin su ne in suka koma ga shan muggan kwayoyi. Wanda a karshe, sakamakon shan muggan kwayoyin shi ne su kashe kansu. Yanda ake samun yawaitan kashe kai a tsakanin ‘yan Nijeriya a ‘yan shekarun nan, abin ya wuce a ce na bangare guda ne kadai, lamarin ya rutsa da, tsaffi da matasa, maza da mata, daga kowane bangare na Addinai, kuma kowace kabila.
Xaya daga cikin irin wannan abin takaici da ban tsoron da ya faru a legas kwanan nan, bayan da wata mata ta rasa ‘ya’yayenta biyu a sakamakon ginin wata makaranta da ya rusa da su, sai ita ma uwar wacce take da ‘ya’ya uku ta kwankwadi maganin kwari ta kashe kanta.
A daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke cikin jimami da firgita kan wannan mummunan lamarin, sai kuma ga wani labarin na wani Malamin Jami’a da yake koyarwa a wata Kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya, shi ma ya kashe kansa. In a yi ta lissafi ne, jerin yana da yawa, zai kuma ci gaba ne da karuwa matukar ba wani muhimmin mataki aka dauka na dakatar da hakan ba a cikin gaggawa. Bai kamata gwamnatocin tarayya da na Jihohi musamman, su ci gaba da nuna halin ko-in-kula ba a kan yawaitan ‘yan kasa da suke kashe kansu.
Wannan Jaridar ta yi imani da cewa, an jima da rushe tsarin ‘yan’uwantaka da ke tsakanin ‘yan Nijeriya, ta hanyar rungumar irin rayuwar baki Turawa, wanda ake tutiya da ita a halin yanzun. Wannan bakuwar tsarin rayuwar wacce take koyar da komai kanka ka sani, tare da rashin nuna wata damuwa a kan abin da yake shafan makwabcin ka. Tsarin nuna ma juna ‘yan’uwantaka ta mutuntaka, tuni an yi watsi da shi.
Hakanan, ya kamata gwamnatin tarayya ta hanzarta daukan matakai wajen gyara lamarin rayuwa da jin dadin ‘yan Nijeriya. A kuma shiga yin fadakarwa sosai a kan hadarin da ke tattare da tunanin mutum ya kashe kansa a kafofin yada labarai.
Sannan ya kamata gwamnati ta bude wuraren tuntuba da bayar da shawarwari nagari a duk ofisoshin lafiya da ke kananan hukumomi, inda duk wadanda suke cikin damuwa za su je domin samun shawarwari nagari.
A kuma tsananta tare da karfafa yaki da siyar da muggan kwayoyi. Duk hukumomin tsaro da sauran kungiyoyin da aka dora masu alhakin gudanar da wannan aikin, kamata ya yi su kara azama da himma a kan aikin na su. Ba kawai su tsaya ga kwace muggan kwayoyi din ba, su tabbatar da sun hana samar da su da dillancin su da kuma siyar da su.
Muna kuma neman shugabannin Addinai, Sarakunan gargajiya da su yi wa magoya bayan su bayani sosai, su taimaka masu wajen kwantar masu da hankali, su kuma ba su tabbacin akwai fata mai kyau a nan gabakadan da izinin Allah.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!