Connect with us

LABARAI

Yau Sama Da Mutum Miliyan Biyar Ake Sa Ran Za Su Halarci Maulidin Inyas A Abuja

Published

on

A yau Asabar ne ake sa ran akalla mutane miliyan biyar (5m) cikin har da shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari da shugaban kasar Senegal hadi da wasu jiga-jigan malaman addinin Islama hadi da Sharifai da Shehunai za su hallarci babban bikin maulidin tunawa da ranar haihuwar Shehu Ibrahim Nyass da za a gudanar a ranar yau Asabar 6 ga watan Aprilun 2019 a babban filin wasanni ta Stadium da ke birnin tarayya Abuja.
Maulidin na bana an tsara gudanar da shine domin tunawa da ranar da aka haifi babban Shehin darikar Tijjaniyya wato Shehu Ibrahim Nyass, inda taron na bana 2019 aka kawatar da tsarinsa.
A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da mai magana da yawun Gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Ahmad Mohammed Saka ya sanya wa hanu hadu da rabar wa ‘yan jarida a Bauchi jiya, ya shaida cewar babban taron maulidin ya fara kankama da halartar manyan baki ne tun a ranar Laraba 3 ga watan Aprilun wannan shekarar, kana ya ce an shafe kwanaki uku wajen gudanar da ‘Makon Shehu’ wanda ya ce zai tun a ranar Laraba zuwa Juma’a aka gudanar, inda jawabai da makaloli kan rayuwar Shehu Inyas suka gabata daga bakunan manyan malamai.
Sanarwar ta kara da cewa, Makon Shehun din ya gudanuwa ne da gabatar da jawabai daga bakin manyan malamai wanda suka yi a cikin babban masallacin kasa da ke Abuja, ya ce, sarakuna, limamai daga sassan Nijeriya da kasashen waje ne suka halarta da gabatarwa.
A cewar Sanarwar ta Ahmad Saka, shugaban darikar Tijjaniyyah Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shaida cewar gidauniyar tasace ta shirya wannan bikin ta kasa da kasa domin karrama Shehu Ibrahim Nyass da mutunta girma da daukakan da Allah ya masa, kana ya shaida cewar an shirya taron kuma domin koyar da jama’a muhimman darusa daga cikin rayuwarsa domin ya zama abin koyi.
Sanarwar ta ce Sheikh Dahiru ya roki matafiya da jama’an tsaro da su yi kokarinsu wajen fahimtar wannan taron da irin cinciridun jama’an da za su gani suna zirga-zirga a lokacin bikin maulidin domin kauce wa shiga hakkin wasu.
A cewar sanarwar da Ahmed Muhammad ya aiko mana, ya ce, shugaban kwamitin shirya bikin Maulidin na wannan shekarar, Alhaji Ibrahim Sheikh Dahiru Usman, yana cewa manyan malamai daga kasashen Morocco, Algeria, Mauritania, kasar Amurka, Mali, Egypt Senegal, Sudan, Ghana, Cameroon, Niger da wasu kasahen Larabawa hadi da wasu kasashen Afurka ne ake tsammanin halartowar baki daga cikinsu domin halartar wannan maulidin.
Ya kuma shaida cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kasance babban bako a wajen taron na maulidin shehu Inyas na bana da zai gudana yau Asabar a birnin tarayya Abuja.
Ya ce, Khalifar Shehu Tijjani, Sheikh Muhammadul Kabir, da Khalifan Sheikh Ibrahim Nyas, Sheikh Ahmad Tijjani Nyass, da kuma babban Limamin masallacin Sheikh Ibrahim Nyass, Sheikh Tijjani Aliyu Sise, da kuma Sheikh Sherif Umar Hafid sune za su gabatar da jawabai a wajen bikin na makon Shehu, inda wasu ma daga ciki da wajen kasar nan za su tofa albarkacin bakinsu kamar yadda sanarwar ta ce.
Ya ce taron zai kawo karshe dai da gudanar da babban biki a dandamalin wasanni ta Stadiyum da ke Abuja a ranar Asabar 6 ga watan Afrilun 2019.
Alhaji Ibrahim ya ce Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh al Husseyn gami da wasu manyan malamai na Darikar Tijjaniyya ne za su gabatar da jawabai a wajen taron na ranar Asabar da za a yi a Stadiyum da ke Abuja.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!