Connect with us

RIGAR 'YANCI

Zaben Kano: Mun Gama Shirin Kare Kanmu A Kotu, Cewar INEC

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta reshen Jahar Kano ta kammala shiryawa tsaf don kare kanta a kotu da zarar kotun ta nemi su a kan wani korafi ko wata kara da wani dan takara ko wata jam’iyya ta kai su a zabubbukan Kano da a ka gabatar na 2019.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin daraktan yada wayar da kai na hukumar kuma babban kakakinta a jihar, Malam Garba Lawal, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a ofishinsa bayan kammala mika takardun shaidar cin zabe da gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da ’yan majalisar jihar guda 40, wadanda su ka hada da ’yan majalisa daga jam’iyyar APC su 26 da kuma jam’iyyar PDP 14 a majalisar dokoki ta jahar, inda kuma a ka mikawa gwamnan tare da mataimakinsa da ’yan majalisar jiha na APC a filin wasa na tunawa da tsohon shugaban kasa, Marigayi Sani Abacha, inda daukacin wakilan PDP su ka kaurace wa taron bikin, amma su ka karbi takardunsu a ofishin da ke Kano, kamar yadda wata majiya ta tabbatarwa LEADERSHIP A YAU.
Ya ce, “al’ada ce kuma abu ne da a ka saba, ba baQo ba cewa duk lokacin da a ka gabatar da zabe wasu su kan nuna rashin gamsuwarsu da zabe kuma su garzaya kotu kamar yadda doka ta ba su damar yin hakan kuma ba laifi ba ne kowane dan kasa ya nemi hakkinsa da damar sa a gaban kotu kamar yadda tsarin mulki ya tanada ya kuma yarda a yi hakan.”
Ya ce, wata karar ko wani korafin ya na samu asali ne daga zaben fidda gwani a matakin Jam’iyya wanda ake kira da Primary Election da turanci to kuma a wani irin mataki ne da zarar an kai kara koto to koto takan nemi hukumar zabe ta INEC kuma mu mukanje ne mu ba da shaida kuma mu ka re kanmu akan wani abu da mai kara yayi zargi dan haka yanzu ma mungama shiryawa tsaf dan ka re kan mu a koto da zarar bokatar hakan ta tasu an neme mu a koto za muje dan kare kanmu.
Haka kuma ya yabawa dukkanin masu rowa da tsaki a harkar gudanar da zabe tundaga kan al-ummar musulmi da abokan zaman su wajen yin addu’a na kamala zabe kamar yadda Allah ya nuna wannan lokaci na godanar da zabe yadda ya kamata sakamakon taka rawa ga dukkanin masu ruwa da tsaki sukayi inda kuma yayi addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano da Qasa baki daya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!