Connect with us

KASUWANCI

Majalisar Dattawa Ta Bai Wa AGIP Tabbacin Aikin Danyen Mai Na Dala Biliyan 13.5

Published

on

Kwamitin Majalisar Dattawa akan kayan da ake sarrafawa a Nijeriya ya baiwa kamfanin mai na Agip dake gudanar da ayyukan sa a cikin kasar da kuma sauran masu ruwa da tsaki a fannin tabbacin goyon bayan kwamitin.
Har ila yau, kwamitin ya kuma bayyana aniyar sa akan zagewa wajen aikin danyen mai na dala biliyan 13.5 na Zabazaba.
Shugaban kwamitin Sanata Solomon Adeola ne ya bayar da tabbacin a cikin sanarwar da mai bashi shawara a harkar yada labarai Mista Kayode Odunaro ya fitar a Abuja.
Adeola ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Talatar data gabata a wani taro da kwamitin sa kamfanin mai na Oando and Nigeria da kuma kamfanin NNPC suka shirya.
Taken taron shine, “ Gudanar da bincike da samar da ci gaba ta tannin fasahar zamani a fannin mai da iskar gas.
Adeola ya yi alkawarin cewar majalisar zata mayar da hankali akan aikin da a yanzu ake jiran umarnin zuba jari akansa kuma aikin mai kasance shine na farko ga hukumar da take sanya ido akan kayan da ake sarrafawa a Nijeriya NCDMB da kuma kwamitin na majalisa dake sanya ido akan kayan da ake sarrafawa a Nijeriya.
Acewar sa, aikin shine na farko tun lokacin da kudurin sarrafa kayan a cikin gida Nijeriya ya zama doka a 2010 kuma hakan zai kara yawan yan Nijeriya wajen ahiga fannin mai da iskar gas.
Ya ce, majalisar tana ra’ayi akan aikin, musamman ganin zai baiwa dimbin fannin Nijeriya damar shiga fannin mai da iskar gas a kasar nan.
Adeola ya yabawa kwamitin na majalisar don samar da kwararrun wajen gudanar da aikin kamar Zabazaba.
Ya ce, a matsayin mu na wakilan yan Nijeriya ya zama wajibi a gare mu wajen tabbatar da yan Nijeriya sun amfana kai tsaye wajen sarrafawa da kuma hakar danyen mai a kasar nan.
Acewar sa, fannin tuni ya samu nasarar samun kashi 28 bisa dari na kayan da ake sarrafawa a Nijeriya kuma nufin shine ya kai had zuwa shekarar 2027, don a kai kashi 70.
A jawabinsa tunda farko, mataimakin shugaba kuma Manajin Darakta na kamfanin NAOC Mista Lorenzo Fiorillo ya ce, kamfanin a shirye yake wajen bayar da tasa gudunmawar don’t ciyar da tattalin arzikin Nijeriya.
Ya ce, kamfanin yana bin dokar sarrrafa kayan a cikin Nijeriya a fannin danyen mai da iskar gas, inda ya kara da cewa, an shirya taron me don kara samar da fasaha ta zamani wajen aikin sarrafa danyen mai da iskar gas a Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!