Connect with us

KASUWANCI

Tattalin Arzikin Najeriya Ya Na Raguwa, In Ji Bankin Duniya

Published

on

Bankin Duniya ya sanar da cewar, tattalin arzikin Nijeriya yana kara raguwa tun daga shekarar 1995, inda ya ci gaba da rauwar har zuwa shekarar 2018.
Bankin ya sanar da hakan ne a cikin sabon rahoton sa da ya fitar na tattalin arzikin nahiyar Afkrka akan kokarin da yankunan na nahiyar Afirka sukayi akan tattalin arzikin su.
A cewar Bankin, anyi amfani da mizani na auna tattalin arzikin don taimakwa wajen gano nasarori da gazawar akan kokarin tattalin arzikin kasashen dake cikin nahiyar ta hanyar mayar da hankali akan tattalin arzikin da kuma hada-hadar kudi.
Masu fashin baki sun bayyana cewar, hakan ya hada da yin dogon nazari akan tattalin arzikin kasashe 44 dake cikin nahiyar ta Afrika tun daga shekarar 1995 zuwa shekarar 2018.
Ma’aunin da akayi amfani dashi akan ko wacce kasar su 44 dake a cikin nahiyar ta Afrila akan tattalin arzikin su, Bankin na Duniya ya ce, sun hadada, kudin shiga da kasashen suke samu, gudanar da ayyukan ci gaba, samar da ayyukan yi da kuma yadda ake gudanar da hada-hadar kudade a kasashen.
Sauran sun hadada, yawan basussukan da ake bin ma’aikatun gwamnati da karin bashin da ake bin kasashen da kuma sauran basussukan da ake bin su a kasashen duniya dana cikin gida.
A cewar Bankin, almomin na karshe sun hadada, gudanar da harkar mulki, yaki da cin hanci da rashawa, karfin iya gudanar da shugabanci, bin ka’ida samar da daidaito a fannin siyasa kaucewa tayar da zaune tsaye da kuma bin doka da oda.
Bankin ya kara da cewa, Iran akkn kwatanta karfin tattalin arzikin daga shekarar 1995 zuwa shekarar 2008 sabanin daga shekafar 2015 zuwa shekarar 2018 .
A cewar Cibiyar Bretton Wood, idan kokarin tattalin arzikin kasar ya ragi saga shekarar 1995 zuwa shekarar 2008 da kuma zuwa shekarar 2015 zuwa shekarar 2018, Nijeriya ta fada a zangon kasar da tattalin arzikin ta ya ragu.
Karuwar tattalin arzikin na cikin gida babu wani sahihin ci gaba, inda ya kai daga kashi 3.5 zuwa kashi 5.4 bisa dari.
A bisa ma’aunin mizani na Bankin Duniya ya sanya kasashe 19 da suka hada da Angola, Burundi, Botswana, Kongo , Comoros , Gabon, Ekuatorial Guinea, Liberia, Lesotho, Mauritania, Malawi, Namibia, Nijeriya, Sierra Leone, Eswatini, Chad, Afirka ta Kudu, Zambia da kuma Zimbabwe.
Wadanan kasashen basu samu cimma wata ci gkba ba kwwat-kwata akan fannin tattalin arzikin su ba daga shekarar 1995 zuwa shekarar 2008 da kuma daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2018.
Alal misali, matsakaicin tattalin arzikin ya ragu daga kashi 5.4 daga shekarar 1995 zuwa shekarar 2008 da kuma zuwa kashi 1.2 bisa dari daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2018.
Bugu da kari, Cibiyar ta Bretton Wood ta yanke yakinin da ta yi na tattalin arzikin Nijeriya zuwa kashi 0.1 bisa dari, inda Cibiyar ta ce, a shekarar 2018, ana sa ran zai karu zuwa kashi 1.9 zuwa kashi 2.1 a shekarar 201, inda kima kaahi 9 0.1 ya ragu a cikin watan Okutobar data gabata.
A na kuma sa ran za’a kara samun karuwar Kazan -kadan zuwa kashi 2.2 bisa dari a shekarar 2020 har ya kai kashi 2.4 bisa dari a shekarar 2021 ganin cewar an kara samun bunkasa zuba jari.
Sai dai, a Nijeriya masank’antu da kuma wanda bai shafi fannin ba, sunci gaba da kasancewa akan kashi 50 bisa dari saboda rashin samun kasuwa akan kayan sa suka sarrafa kuma masu sayen kayan a cikin kasar suna kara Ragusa saboda matsalin tattalin arziki a tsakanin su da ci gaba da gazawa wajen samo masu zuba jari a tattalin arzikin Nijeriya.
Kwarren mai fashon baki a fannin tattalin arzikin a nahiyar Afrika Albert Zeufack yankin zai iya bunkasa tattalin arzikin na shekarar-shekara zuwa kimanin kashi biyu bisa dari, musamman idan an rungumi fannin bayanan fasaha kuma wannan shine chanjin da ake son a samar ga nahiyar Afirka
Shi ma mai magana da yawun Babban Bankin Nijeriya CBN Mista Isaac Okorafor ya ce, CBN a bisa karkashin shugabancin Mista Godwin Emefiele ya bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen cigar da tallin arzikin Nijeriya.
A karshe ya ce, kun san halin da mula shiga a cikin shekaru ukun da suka gabata, Bankin ya yi nasa namijin kokarin wajen daidaita tattalin arzikin Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!