Connect with us

RA'AYINMU

Matsalar Tsaron Zamfara Da Bukatar Zaman Lafiya

Published

on

Sakamakon ci gaba da tabarbarewar tsaro a Jihar Zamfara da kuma kokarin yaki da ta’addanci da ‘Yan ta’adda, ya tilastawa Gwamnatin Tarayya dakatar da masu hakar ma’adanai na cikin gida tare da fatattakar ‘Yan kasashen waje masu hakar ma’adanan ba bisa ka’ida ba ko ta barauniyar hanya. A halin da ake ciki yanzu, ‘Yan Sanda ne ke kula da kafatanin gureren da ake hakar wadannan ma’adanai kamar yadda gwamnati ta ba da umarni.
Kafin daukar wannan mataki, Gwamnatin Tarayya da ta jiha sun gamsu cewa ko shakka babu wannan ta’addanci da ya ki ci ya cinyewa a Jihar ta Zamfara na da alaka kai tsaye da hakar ma’adanai ta barauniyar hanya. Wannan ne ya sa wasu ke ganin wadanda ke amfana ta hanyar hakar wadannan ma’adanai ko kadan hukuncin da Gwamnatin Tarayyar da na jihar ta yi ba zai yi musu dadi ba. Amma a gefe guda kuma, wadanda ke dandana kudarsu ta hanyar karkashe su da raunata su da ake yi babu dare babu rana da aka dauki tsawon lokaci ana yi da kuma sauran ‘Yan Nijeriya masu kishi da son ‘Yan’uwansu, ko shakka babu abin zai yi musu dadi.
Har ila yau, tsauraren matakan da gwamnati ke dauka a halin yanzu kan matsalar tsaron Zamfarar shi ya kamata a ce tuntuni ta dauka. Dalili kuwa, ita ce ke da alhakin kula da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar wannan jiha. Saboda haka lallai ne ta yi iyakar iyawarta wajen ganin zaman lafiya da walwalar al’ummar wannan jiha ta dawo kamar yadda aka saba yi a da. Don kuwa, shi kansa Shugabanci ko mulki na yin tasiri ne a cikin al’ummar da ke zaune lafiya.
Haka zalika, wannan Kamfanin Jarida na nan kan bakarsa ta bayyana damuwa da rashin jin dadi bisa yadda aka gudanar zabubbukan cikin gida a wannan yanki wanda hakan ke kama da kama karya da kin baiwa al’umma damarsu ta zaben irin mutanen da ke da nagarta a wurinsu, aka yi abin da rai ke so na son zuciya da rashin kyautawa, babu shakka yin hakan ya sake taimakawa jihar sake fada wa cikin muwuyacin hali.
Bugu da kari, sanin kowa cewa duk al’ummar da ke kan tsari ko tafarki irin na Demokradiyya kamar Nijeriya, na sa ran samun ‘yanci, fadin albarkacin baki da sauran makamantansu kamar yadda tsarin mulki ya tanadar. ‘Yanci da damar da ‘Yan kasa ke da shi, ya hada da gabatar da bukatun kashin kai musamman akan abubuwan ci gaba da kuma ayyukan raya kasa a kowace fadin jiha ko yanki. Wannan dalili ne yasa mu ma anamu bangaren muka dubi bukata tare da kukan wasu daga cikin al’ummar wannan jiha game da gwamnatocinsu, dalili kuwa halin da Jihar Zamfara ke ciki yanzu ya kai illa masha Allahu. Don haka ya zama wajibi Hukumomin tsaro su hada karfi da karfi wajen fatattakar ta’addanci da ‘Yan ta’adda da ke fadin wannan jiha ko yanki baki daya.
Koda yake a nasa bangaren, Gwamna Yari na iyakar kokarinsa wajen ganin ya dakile matsalar ta’addancin a Zamfara, amma da yake abu ne da ke da alaka da barauniyar hanya ko wajen wannan kasa, yasa dole abin ya fi karfinsa. Duk da haka gwamnan bai yi kasa a gwiwa ba, ya ci gaba da neman yin hadin gwiwa da Gwamnatin Tarayya don kawo karshen ta’addancin a Zamfara.
Wakazalika, Gwamnatin Jihar ta yi kokarin rabawa Jami’an tsaro daban-daban motocin sunturi, daukar ‘Yan Doka na sa kai kimanin 8500, samar da gidajen kwana ga Jami’an tsaro, samar da bayanan sirri ga Jami’an tsaro, ganawa da Sarakunan gargajiya lokaci zuwa bayan lokaci, samar da alawu-alawus ga Jami’an tsaro duk watan duniya da sauran makamantan su duk dai don dakile wannan masifa da ta addabi Jihar ta Zamfara. Saboda haka, mu ma a namu bangaren ba ma goyon bayan abin da ke faruwa musamman a wannan jiha ta Zamfara, Kaduna da kuma Katsina. Muna kuma sake yin addu’ar duk wadanda ke da hannun a wannan ta’addanci don biyan bukatar kansa, Allah Ya ci gaba da tona masa asiri, Ya kawo wa wadannan yankuna zaman lafiya da kasa baki daya.
A karshe muna sake kira ga gwamnati wajen ci gaba da jajircewa wajen magance matsalolin tsaro musamman a wannan yanki na Zamfara. Dole ne a ci gaba da daukar tsauraran matakai da hukunta duk wadanda aka samu da hannu a cikin wannan ta’addanci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!