Connect with us

TATTAUNAWA

Bakuwarmu Ta Mako: Rashin Tarbiyar Na Cikin Abin Da Ya Kawo Tabarbarewar Ilimi A Nijeriya —Farfesa Binta

Published

on

Gabatarwa
Sunana Farfesa Binta Abdulkarim, ni malama ce a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, ina kuma koyarwa ne a fannin koyar da kimiyya da fasaha, wato Science Education kenan, a takaice dai duk wani malamin da zai koyar da ilimin kimiyya da fasaha mune malamansu.

Za mu so mu ji takaitaccen tarihinki.
To Alhamdulillahi, ni dai haifaffiyar Anchau ce, da ke karamar hukumar Kubau ta jihar Kaduna . Da muna Ikara ne sai aka raba ta zama Makarfi da Ikara da Kubau, to sai Anchau ta dawo sashen Kubau, amma a Kaduna na girma, tun ina yarinyata a Kaduna na girma nan Kawo, a nan na yi firamare n agama a shekara ta 1973 da muka kammala kuma sai na shillo Soba, mu ne daliban farko da muka fara shiga makarantar a 1969.
Daga nan kuma sai na tafi makarantar nan ta share fagen shiga jami’a, wato CAS, to a lokacin an bude ta ne saboda dalibai ba su cin jarabawa sosai ta zuwa jami’a, kuma mu ne daliban rukuni na biyu da muka je. Daga nan kuma sai na shillo jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya na koyi ilimin kimiyya, har zuwa digirina na uku, har na zama Farfesa, duka dai a wannan jami’a.

Kalubalen Dana Fuskanta
Na fuskanci kalubale masu yawa, a lokacin da muka taso muna yara akwai matsalar Kudu da Arewa, lokacin ne aka fara wannan hatsaniyar rashin jituwa tsakanin Iyamurai da Hausawa. Idan muka tashi sai mu ga an kwashe mu a kai mu wasu gidajen a boye mu, sai muna ta tambaya a’a me ke faruwa, ashe lokacin ne aka kashe Sardauna.
Mun razana sosai sai na tashi da tsoron cewar ai idan harsuna biyu ko uku suka yi zamantake wa ai fada ake yi, to ka ga kalubalena na farko ke nan, tun ina yarinya, don na razana sosai, da na ga jirgin sama sai in razana, sai na dauka yaki ake yi.
Amma da tafiya ta yi tafiya, sai kuma na lura cikinmu ma Hausawa Musulmi, ana kyamatar ilimin boko, duk inda muka je sai a rika cewa ga su nan karuwai, ‘yan boko, bokoko a wuta, tun ba ma in mun je Anchau ba, a yi ta binmu, kamar dai an ga dodanni, to in na tafi gida sai in ce baba ga fa abin da ake cewa, sai ya ce in yi hakuri. Ba su gane ba ne, domin da sun gane ba za su rika kiranmu ba wannan suna ba.
Sai ya zamana ba mu cika sakin jikinmu a cikin jama’a ba sai mun koma Kaduna. A Kaduna ba wani mai kyamar wani amma da zarar mun tafi Anchau sai harka ta canza saboda kyamatarmu da ake yi.
Bayan wannan ya shige sai kuma kalubale na uku, ita kanta zaman rayuwar sai na lura cewar jama’a su ba gaskiya suke so ba, a duk inda ka zauna in ka fadi gaskiya to abu biyu zai faru, ko wasu su yarda da kai ko wasu su dauke ka mahaukaci. To tunda na ga haka sai na ce a’a, to yanzu karya zan ta yi wa jama’a su yarda da abubuwan da nake yi ko kuma in karbu ga jama’a ko kuma in yi shiru ne komai ma ya rushe ya lalace?
To ka ga abu ukun nan, rashin kwanciyar hankali da kyamatar mutum, da kuma gurgunta alkiblar mutum, shi kanshi ba karamin kalubale ne a halin rayuwa ba,
A yanzu haka idan na ga gungun jama’a har shakkar magana nake, domin wasu ba fa gaskiya ake so ba. Wasu sun fi so a yi karya zane da riga, idan kuma karyar namiji ne a yi mai riga, da wando da hula har da rawani.
Batun karatu ban samu kalubale ba, don yawanci ma wasu da suke a gabana na zo na cim musu a makaranta. In kuma ka gan ni a cikinsu za ka yi tunanin ta yaya na zo na cim musu a karatu? Ban samu kalubale a wurin karatu ba gaskiya.

Nasarorin Da Muka Samu
Na farko dai nasara ta daya, a gida, an ba mu ‘yancinmu yi duk abin da muke so amma fa akwai ka’idoji, in lokacin ibada ya yi to ba mu isa ba dole ne mu zo mu yi ibada fa, an ba mu ‘yancin hulda da kowa amma fa dole mu girmama ko waye muke hulda da shi.
Sannan sai na shallake wannan shingen yarintar ya zamana na san abin da duniya ke ciki, sai na lura cewa duk abubuwan da na sa a gaba ci gaba muke yi, wajen karatu ba matsala, neman aiki ba matsala, koyarwar da muke yi ba haufi ko kadan, ci gabana, na tafiya yadda ya kamata. Ai kuwa mun gode wa Allah, Alhamdulillahi, kuma zan kara da cewa batun wajen harkar jama’a ba mu da matsala, sai dai wasu ‘yan karya, dama ni in na san mutum dan karya ne ko inuwansa ba na kallo bare shi kansa, ba wasu kalubale da zan ce za su kawo min matsalar rayuwa.

Bambancin Ilimin Da Da Na Yanzu
Ai abin ma in ka ji tarihin sai ka yi wa ‘yan bana kuka, wato daliban nan, ina tausaya musu, tun daga firamare zuwa makarantun share fagen shiga jami’a da ‘yan jami’an kansu. A zamaninmu, mu kam alkiblarmu karatun ne kawai. Ba abin da ba a yi mana ba, gwamnati ta lura da mu. Yanzu kila ko don an ce in dambu ya yi yawa ba ya jin mai, shi ya sa daliban ke wahala.
A nan kuma zan kara da cewa yaranmu abin tausayi ne, karatu fa sai in ana da tarbiyya, yawancin yaranmu ba su san in sun ga na gaba su gai she shi ba, ba su san su natsu ba a waje, ba su san ka’idar al’adunmu da zamantakewarmu na Arewa ba. Kullum ana kuka da dalibai kanhaye-shaye da shiga kungiyar asiri miamakon su fuskanci katatu. Rashin tarbiyya ita ta kara tabarbarewar.

Farfesa batun iyali fa?
Eh, ina da ‘ya ‘ya biyar, biyu mata, uku maza. Daya matukin jirgin sama ne, daya kuma hamashakiyar mai aikin noma ce, a fannin tsirrai wanda ake cewa canjin jinsin tsirrai wato “Plant Genetics” tana Kanada, tana aure a Kanada, biyu suna Germany, daya yana karatunsa na digiri na uku, daya yana na biyu shi kuma. Dayar kuma tana karatun hako ma’adanai wato A’isha, ita ce.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!