Connect with us

LABARAI

Wanda Ya Jagoranci Juyin Mulkin Sudan Ya Yi Murabus

Published

on

Tsohon Ministan tsaron kasar Sudan wanda ke rike da madafun ikon kasar ya mika ragamar mulkin kasar ga daya daga cikin manyan hafsan Sojan kasar mai suna Abdel Fattah Al Burhan Abdelrahmane.

Majalisar Sojin kasar ta Sudan dai tun bayan kifar da Al Bashir ta ce ba za ta mika hambararren shugaban kasar Omar al-Bashir da ke fuskantar tuhume-tuhumen da suka shafi kisan kiyashi da laifukan yaki ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ba wato ICC.

A jawabin da ya yi wa taron manema labarai, shugaban kwamitin siyasa na gwamnatin sojin Sudan, Laftanar Janar Omar Zain al-Abdin ya ce, a halin yanzu, hambararren shugaban yana hannunsu, yana mai cewa, a matsayinsu na sojoji masu tafiyar da al’amura a kasar, ba za su mika shi ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ba.

Sau biyu kotun hukunta manyan laifuka ke aike wa da takardar neman a mika mata tsohon shugaba Omar al-Bashir, sakamakon laifukan yaki da ke ta hakkin bil’adama da ta ce ya aikata a yankin Dafur a tsakanin shekarun 2003 da 2008.

A jiya Juma’ar nan, jagoran Majalisar Soji, wadda shi ne Ministan Tsaro a gwamnatin al-Bashir, Awad Ibn Ouf, ya sanar da sauka daga mukamin nasa, bayan haka ya yi kashedin cewa, ko kadan ba za su lamunci birkita tsaro a kasar ba, bayan masu zanga-zanga sun yi kunnen-kashi da dokar takaita fitar dare don ci gaba da zaman-dirshen na neman a dawo da mulkin farar hula ba tare da bata lokaci ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!