Connect with us

SIYASA

Yadda Na Tika PDP Da Kasa A Zaben Kano -Gwamna Ganduje

Published

on

Wannan fassarar wani sashe ne na hirar da ‘Jaridar Daily Trust’ ta ranar Lahadi 1 ga watan Sha’aban, 1440 Bayan Hijira daidai da 7 ga watan Afrilu, 2019 ta yi da Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Khadimul Islam (OFR). Ga yadda hirar ta kasance. A sha karatu lafiya:

Mai girma Gwamna shin ka fara shirye-shiryen rantsuwa ne a karo na biyu, bayan nasarar cinye wannan zaben da a ka gudanar?
Ganduje : A’a ban fara wannan shirin ba tukuna. Sai dai abin da ya fi muhimmanci shi ne na fara shirye shiryen ire-iren ayyukan da za mu cigaba da yi wa jama’a da kuma ire-iren manufofin da su ka dace da mu cigaba da su da kuma sababbin da za mu kara fito da su.
Haka nan kuma mu na ta kokarin ganin halin da dukkanin ma’aikatunmu ke ciki. Saboda mu kara tabbatar da wajen da za mu dora. Da kuma wuraren da za mu kara yi wa kwaskwarimar ayyuka saboda samuwar tabbataccen cigaban kasa da al’umma.

Lokacin da a ka rantsar da kai a zangon farko, mun ga ka sa jar hula. A wannan rantsuwa kuma ta biyu akwai wata kalar hula ce daban da za ka sa ko kuwa?
Ka na maganar Kwankwasiyya ne?

Akwai irin kalar hular Gandujiyya ne?
Ai mu ba mu da wata kalar hula ta musamman da muke amfani da ita. Ya kamata ka san cewa mun fa ajiye jar hular Kwankwasiyya har abada. Mu kuma a namu bangaren, mutum ya na iya yin amfani da duk hular da ya ga damar sa wa. Ba wani zabi na wata kala ta musamman. Ka san da cewa kuwa jar hula ta Kwankwasiyya nine na kirkiro ta?
Akwai lokacin da jirgin kamfen din marigayi ‘Yar Adua yake son zuwa Kano, a lokacin kuma shi Kwankwaso dan takara ne na gwamna, ni kuma ina cikin tawagar neman zaben Goodluck Jonathan, lokacin yana mataimakin shugaban kasa. Ka san ni da Jonathan mu na mataimakan gwamnoni daga 1999 zuwa 2003.
Saboda haka na san shi sosai. Kuma na yi kokarin sanin yadda jihohinmu suke a siyasance matuka a loakcin. Abin da na lura da shi shi ne, mu a nan Kano, mu na da jagorori, misali Malam Aminu Kano. Saboda haka da a ka zo maganar irin kalar kayan da za a sa, sai na bayar da shawarar cewa, ai jar hula wata aba ce da tuntuni an san Malam Aminu Kano irin kalar hularsa kenan.
Kuma ga fararen kaya, sai kawai na ce yakamata mu ma mu sa jar hula da fararen kaya. Ga kuma bakin takalmi. To ka ga yadda abin ya kasance. Da ‘Yar’adua ya zo da mutanensa sai mu ka ba shi irin namu kalar kayan shi ma ya sa. To ka ji asalin yadda jar hular Kwankwasiyya ta fara.

Kwanan nan a ka kammala zaben gwamna a zango na biyu. Me ka ke gani game da wannan zabe?
Amma ai kamata ya yi ka fara tambaya kan zaben zango na farko da a ka fara. Ka san dalili? Saboda zabe na biyu ai daga na farko ya dauko beza.

To me za ka ce game da zaben farko?
Wannan kam cike ya ke da magudi da karya dukkanin ka’idojin zabe wadanda suke a shimfide cikin kundin Hukumar Zabe Ta Kasa. Wanda hakan ne ya sa a ka ce zaben bai kammala ba, sai an je karo na biyu. Idan ba ka manta ba, an soke zaben ne saboda matukar magudin da a ka yi wajen yin zaben.
Ba a yi amfani da katin tantance masu jefa kuri’a ba, an yi amfani da yan daba a wuraren jefa kuri’a. Sannan a wasu wuraren kuma an fasa akwatunan zabe an lalata kayan zabe. Ire-iren wadannan abubuwa ne su ka sa dole zaben a soke shi bai kammala ba. Kamar dai yadda hukumar zabe ta kasa ta yi. Kuma sun hada baki da jami’an tsaro a lokacin wajen tafka wannan abu da su ka yi.
Abin da hakan kuma ya haifar shi ne, kuri’un da a ka soke, sun fi karfin tazarar da a ka samu tsakanin wanda a ka ce ya na gaba a zaben da kuma mai bi masa. Ka ga kenan, ashe idan kawai ka tafi kai tsaye yin tambaya kan zabe na biyu, lallai ka bar muhimman abu wanda ya shafi tarihin yadda ma zaben ya samo asali kenan.
Kuma idan ka lura da kyau za ka iya fahimtar cewar an samu wannan tafka-tafka ta magudin zaben na farko musamman a kananan hukumomi takwas da suke cikin birni. Misali mun cinye ‘yan majalisar Dokoki Na Jihar Kano guda 27 daga cikin 40. Su kuma an ce sun ci 13. Amma fa daga cikin 13 din nan, 8 daga cikin birni suke, wajen da su ka tafka wancan gagarumin magudin.
Idan ka duba zaben can farko kuma na shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya, mun cinye komai dari bisa dari. Mun cinye shugaban kasa da dukkanin Sanatocinmu su 3 da kuma dukkanin ‘yan majalisar wakilai ta kasa su 24. Wannan gagarumar nasara ta sa mutanenmu a ka dan shantake tsammanin cewa wannan nasarar za ta zarce har ga ragowar zabubbukan.
Amma ile, ashe su wadancan sun yi mugun tanadi ga ragowar zaben namu na gwamna da na ‘yan majalisar jihar Kano. Sun yi mugun tanadin magudi gami da dauko ‘yan daba wajen kawo tashin-tashina a wuraren zabe. Haka nan kuma su ka hada da sayen kuri’un mutane.

To yanzu me za ke ce game da zaben karo na biyu na gwamna?
Wannan ai ba ma wani abu ba ne. Ka ga an yi wannan zabe ne a kananan hukumomi guda 27. Amma kuma ba su ci a ko da daya daga cikin wadannan kananan hukumomin ba, saboda kuwa an tashi tsaye an sa ido a kowane waje. Har ta kai ta kawo ma ba su isa su hada baki da wani jami’in tsaro ba.
Misali idan ka kula, a wancan zaben gwamna din na farko, an yi amfani da jami’an tsaro wajen cusgunawa mutanenmu. Ka san sai da ta kai ta kawo fa an cafke mutanenmu. Ciki har da mataimakin gwamna, wanda yake da kariya daga tsarin mulki na kasa. An cafke mana har da kwamishina.
Amma fa da a ka zo yin zabe na biyu na gwamna din, da yake an tsaurara matakan tsaro sai ta kai ta kawo ba sa iya katabus. Sai kawai su ka fara yada farfagandar cewa wai an yi kashe kashe a zaben Kano. Sai su dauko hotunan fada da a ka yi a Rwanda da kuma wasu kasashen da suke fama da matsalolinsu, su dinga cewa wai daga Kano ne wadancan hotunan.
Har yanzu kuma sun kasa fadawa mutane wuri daya da za a gayawa mutane na wanda a ka kashe. Ku je ku bincika ku gani. Idan ka duba rahoton kwamishinan ‘yan sanda da kuma rahotannin manyan mataimakan babban sufeto janar na ‘yan sanda, ba wanda a cikinsu ya nuna wai an samu kisan kai a wannan zaben na biyu na Kano. Sai ka sha mamaki ko ta ina su ka samo wadancan hotunan karyar.
Kawai su na yin haka ne saboda su firgita wadanda suke ba a Kano suke zaune ba. Amma mutanen da ke cikin garin Kano, sun san wadancan hotuna karya ne. Soki-burutsu ne kawai.

Yanzu misali, a cikinku wa ye kan daidai, su PDP sun fi amincewa da zaben farko na gwamna da a ka yi. Ku kuma kun fi amincewa da zabe na biyu na gwamna da a ka gudanar? Maganar wa ya fi kamata a kama?
Ka ga yadda gizo ke sakar kenan. Ai ni da na gaya muku yadda abin ya ke, ba cewa na yi ba lallai sai kun amince da ni. A’a ce muku na yi ku je ku bincika sannan sai ku san me yakamata ku dauka ko ku bari. Misali ni ce muku na yi ku je ku bincika. Su kuma ce muku su ka yi, duk abin da su ka gaya muku wai sai kun yarda da su. Kun ga bambancinmu da su kenan. Ku je ku yi bincike irin na ku na ‘yan jarida mana. Sannan sai ku dogara da bincikenku.

Sun zarge ku da yin amfani da yan ta-da-zaune tsaye wajen hada baki da jami’an hukumar zabe……..
Ka gani ko? Shi ya sa na ce muku, ku je ku yi bincike. Kuma ma ai dadin abin shi ne, ai za a je kotun sauraren kararrakin zabe ko? To ai kuwa da yawa daga cikin tambayoyinku za su samu amsa a wajen.

An ce a lokacin zaben gwamna na farko, kun yi kuka game da kwamishinan ‘yan sanda. Amma takamaimai menene korafinku game da shi?
Saboda ya na ba su kariya ne. Misali ka ga ai ba shi da damar ya kama mataimakin gwamna. Ko kadan ba shi da wannan damar. Saboda kuwa ai ya na da kariyar da kundin tsarin mulki ya ba shi. Ka ga ai kuwa da mun so za mu iya kai karar wannan kwamishinan ‘yan sanda din. Saboda ya keta kundin tsarin mulkin kasa.
Lokacin da mu ka samu labari mutanenmu su na can wajen da a ke tattara sakamakon zabe, sai mataimakin gwamna ya tafi da nufin zai ce musu lallai lallai su bar wajen, shi kuma ba tare da sanin cewa a she tuni a ka tarwatsa su ba. A daidai wannan lokaci kuma sai a ka bar ‘yan adawa su ka shiga wajen. Saboda haka mataimakin gwamna ya na shiga sai kawai ya fada hannun ‘yan adawa.
Ka ga ai kuwa wannan ba wani abu ba ne illa nuna bambanci da fifiko tsakaninmu. Akwai dan majalisar tarayyarmu tare da shugabannin kananan hukumomi su biyu da a ka hada da su a ka kame. Amma ko mutum daya daga bangaren jam’iyyar adawa ta PDP ban ji an ce an kama ba. Ka ga kuwa wane irin abu ne wannan?
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!