Connect with us

TATTAUNAWA

An Samu Karin Fahintar Juna Tsakanin Musulmi Da Kirista A Jihar Kaduna –Fasto Y D Buru

Published

on

Fasto Yahanna D. Buru sanannen mai wa’azin addnin Kirista ne a jihar Kaduna, ya kuma shahara ne saboda kokarinsa na tallafawa al’umma da kuma tsaya da ya yi don ganin an samu hadin kai a tsakain bangarorin addinai a kasar nan da kuma fafutukan ganin an samu dawawwamen zaman lafiya a jihar Kaduna dama Nijeriya gaba daya. Editanmu Bello Hamza, ya yi tattaki zuwa gidansa dake unuguwar Sabon Tasha a cikin garin Kaduna inda ya tattauna da shi a kan harkokin gwagwarmayarsa da kuma irin tasirin da harkokin nasa ya yi a rayuwar al’umma, ga dai yadda hirar ta kasance.

Za mu so ka gabatar mana da kanka?
Sunana Fasto Yohanna Y D Buru, ni ne Shugaban Peace Rebibal and Reconciliation Foundation of Nigeria, Kungiyar farfado da zaman lafiya, da sasantawa tsakanin Kiristoci da Musulmi da wasu mabanbanta addini na Nijeriya, tare da yardar Allah kuma kuma ina aikin Fasto a Christ Ebangelical fellowship, a nan garin Kaduna a Gbagi billage, nine kuma wakilin Human Right Agency a Nijeriya wato hukumar kare hakkin dan-adam a nan Nijeriya. Wadannan mukamai guda uku da Allah ya albarkace ni dasu, na kuma kasance Shugaban kungiyoyin a nan Nijeriya.

To bayan haka muna so ka gabatar mana da takaitaccen tarihin rayuwarka
To kamar yadda na fadi sunana, wato Fasto Ya D Buru, ni mutum Jaba ne daga cikin garin Kwai anan cikin garin Jihar Kaduna. Sunan babana Anthony Buru, ko kuma Anthony Duci Buru, sunan Mama Ladi Hassan, dukkansu mutanen garin Kwai ne, kuma an haife ni a garin Kwai ne, amma na girama a nan Badarawa cikin garin Kaduna fiye da shekara 40 yau, na girma nan cikin birnin Kaduna, yanzu ina da shekara 52 zuwa da uku. Na yi makarantar Firamare ana cikin gari Kwai anan Zuru wato unguwar Madaki a cikin garin Kwai Arewa cikin gari Kwai. Na gama Firamare sai na dawo garin Kaduna, sannan na koma GSS Kagoro. Amma kafin GSS Kagoro na yi Odford Professional Training Centre, a Unguwar Dosa nan kasuwar Sati da kuma Barawa a Karaye Road, a ka tayar da makarantar zuwa nan, daga nan na zo na yi Sikandire a garin Kagoro.
Abin mamaki da yi Sikandire a Kagoro, na je na yi Pre Mok na yi Mok da GCE duka na yi Sikandire wanda bai wuce watanni takwas da kwanaki 11 ba, na yi Pree Mok ne kadai na yi GCE a nan Kagoro cikin 1987 a nan Kagoro mune aji na karshe a wanda suka yi aji biyar. Daga nan ban kai shekara ba Allah y aba ni aiki, na fara aiki da Kotu, na fara aiki da High Court Of Justice Kaduna State.
Na fara aiki da su ranar 3/3/ 1988, a nan Gwado-gwado Area Court, karkashin Kafancan East. Daga baya na dowo Kaduna a 1991 na ci gaba da aiki a nan kotun Majistiri dake Daura Road, to daga nan a 1996 na yi kwas a nan Staff Debelopment Center a 1992, daidai lokacin ne aka yi rikicin Zangon Kataf, to ina cikin wannan kwas din ne, daga 19196 na samu Admision zuwa Seminary, sai na koma Saminar a Ekwa Church a Seminary Jos na karanta Tauhidin Addinin Kirista, na yi Difloma na zo na yi Digiri, daga nan na dawona bar aiki a shekarar 2000 gaba daya, na bar aikin Kotu na shiga aikin Fasto, a aikin Fasto na kula ne akwai marayu da gwauraye, domin na ga su masu bukata ne, ya kamata a tausaya masu saboda irin wahalar da suke sha.
To tun daga wannan lokacin ne nake ta gwagwarmayar na kwatowa mutane hakkinsu, musamman talakawa wadanda suke shan wahala ko suke wulakanta a hannun wadanda suka fi su karfi, ina wannan aiki na Allah idan na ga na dan samu wani abu komai kankantarsa ina kokari na ga na taimaka masu na taimaki ‘ya’yansu idan akwai wanda ya zo da bukata sai a taimaka masa, to haka nan a fara aikin har ya zo ya zama ministry, aka ce bai kamata a ce kana yin aiki haka bai zama ministry ba, to shi ne na fara aikin Fasto gadan-gadan a 2004 a budadiyyar gidan Yarin Kaduna Ta Kudu a nan Telebision.
To Minstry ta fara bunkasa har ta kai ga matsayin da yake yau, kuma na fara yi ne da mutane kalilan har aka kai ga wannan yanayin da muke ciki. A cikin haka ne na ga dadadden tarihi na rigingimu da na sani cikin garin Kaduna, sai na ce ba wai haka kawai zan yi aikin Fasto ina ganin mutane cikin wannan hali ba, ya kamata na kokarta na ga yadda zan wanzar da zaman lafiya. To sai da ya kai ga na kafa kungiyar Peace rebibal and reconciliation Foundation don wanzar da zaman lafiya, da sasantawa, wanda a zanyu ta kai shekaru shida yau cir, kusan mun shiga ta bakwai da kafuwa.
To lokacin da aka yi fadan Kasuwar Magani tsakanin Adara da Gbagi da Hausa Fulani a kan gona, shi ne ya kai har zuwa yau din nan, daga wannan bangaren abin ya rikide ya zama wani abu daban, to shi yasa na tsaya na ce, dole zan kawo wannan gudunmawar. Abubuwa da yawa sun faru, to daga nan ne na koma na yi Digiri na biyu a Jami’ar Sojoji wato nan ‘NDA Postgraduate School’ ta Kaduna, na yi digiri na na biyu ‘Masters Digree’ nawa, yanzu ma ina International Affairs in a strategy studies.
Na yi Digiri na farko a fannin Tauhidin Kirista, na yi Difloma, na yi kwasa-kwasa, na kuma samu tafiya zuwa kasashen waje, na je Kasashe daban-daban, na je a matsayin jakadan wanzar da zaman lafiya, na je taron kungiyar kare hakkin dan-adam a Kasar Turkiyya, na je Kasar Iran, na je Kasar Isara’ila, na je Kasar Misra.
A kan maganar wanzar da zaman lafiya, na je Kasar Malta, na je kamar su Nijar ba sau daya ba ba sau biyu ba na kai tawaga, Musulmi da Kiristoci mun je mu koyi abubuwa don mu zo mu aiwatar da su, mun je su Benin Republic, da wasu Ksashen makotanmu duk munje wurinsu, ban da aikace-aikace na Nijeriyar a nan, in aikace-aikace Nijeriyar nan ne sunanan wasu ba zan iya tunawa da su ba, domin ina yi don Allah ne kamar yadda wata ta tambaye ranar Juma’a wai ina da niyyar na shiga siyasa ne? na ce mata ban taba tunanin ba tun ban zama Malamin Addini ba, kuma yanzun ma ba na tunani yin siyasa. Amma son jama’a su samu zaman lafiya ne, don a samu zaman lafiya ta yadda Musulmi da Kirista za su samu zaman lafiya, a samu tsawon zamantakewa, kyakkyawar mu’amala don ci gaban Kasarmu gaba daya, a kwana a tashi a ga wata rana mu ne gaba a duniya wajen, kowa ya fahimci dan’uwansa.
Kuma maganar mu’amalata da Musulmai, ina son in gaya maka kawai dai Allah ne bai kaddara ba, amma tun ban zama Kirista ba ina son zama Musulmi, amma bai kaddara ba, dogon labari ne, kuma ba wani musulmi ne ya zo ya yi min wa’azi ba, a’a mu’amalata da Musulmai ce kusan shekaru 35 zuwa 36 zuwan yanzu tun ina ji da kuruciya na so na zama Musulmi domin mu’amalata da su.
Kai har da na bar aikin ma, na shirya zuwa don shiga Collge of Arabic Studies dake Kano ta wajen unguwar Gyadi-gyadi, farkon dai shiga Kano din nan, sai Allah bai nufa ba, rashin lafiya ta kama ni, wannan dalilin kenan da tuntuni ni Musulmi ne. Kuma abin da nake yi din nan kamar gado ne, na san Kakana farin sani, kuma na kusanci Kakana haka nan yake yi da mutane ya rika taimaka masu.

Ya sunan kakan naka?
Sunan Kakana Buru, to kuma sai na babana ya ninka abin da Kakana yake yi, sai baban nawa yake bani labari cewa, ai Kakansa ma haka yake, mutane za su taru a gidansa a dafa abinci, suna noma, sai dai kudi ne ba su da shi, ba su yi ilimin zamani ba amma in dai maganar abinci ta zo to za a ba wa mutane, haka dai babana ya gada wurin babansa, babansa shi kuma ya gada wurin kakansa, ni kuma na gada wurin kakana, to saboda haka wannan abin na cikin jini nane, wallahi wani lokacin in kazo nan gidan za ka ga babu wani abu, amma ba zan iya na hana mutum abinci ba, kuma ina yin wannan abu ne don ina son naga jama’a sun zauna lafiya da juna don a ci gaba.
Wasu suna tambayata har Musulmi suna cewa, mai ya sa kake yi wa Manzon Allah SAW Mauludi? Na ce masu kaunar zaman lafiya, kaunar Manzonku ne ya sa na yi wannan. Bayan haka mene, haramun ne, Mauludin Manzon Allah? A’a ba haramun ba ne, ai ina yin nawa Mauludin na Annabi Isa Alaihissalam, in so samu ne ko wane Annabi zan yi masa, babu wanda ba ya neman albarka, ina neman zaman lafiya ne, bana kyamar addinin mutum ba na kyamar mutum, ina kyamar muguwar halayyar mutum, ko abin da yake kawo mana rashin zaman lafiya, duk abin da zai kawo mana zaman lafiya da ci gaba zan yi kokarin ganin na kawo shi.

Ka yi maganar rikicin Kasuwar Magani, wani tasiri kungiyarka ta yin a kawo zaman lafiya?
Wato a duk lokacin da ake maganar rigingimu a duniya ban taba sani 1980, ba jiyau ba ne ni ganau ne abin da ya faru a kasar nan ne, tun daga wannan lokaci na tsani, na kyamaci maganar rashin zaman lafiya. Maganar Kasuwar Magani kuwa a ce Hausawa Fulani ko Adara, Gwari, Gbagi, suna fada a kan gona, na ce ga gonaki can a kasar Jaba su je su diba mana, har za a tsaya a na fada a kan wata gona ana kashe-kashe da kone-kone, abin ya dame ni duk abin da ake yi yau to zai koma kasan magani, to shi ya sa in dai aka wannan maganar sai na yi maganar Kasuwar Magani.
1980 tsahon shekara 40 saura shekara guda cir, amma ana ta rigima a wannan wurin an kasa magance wannan abin, gaskiya akwai damuwa. Abin da ya faru a kan gona ne, to daga lokacin ba a wuce shekara daya ko biyu ba, sai maganar Maitasine a Kaduna, ina Badarawa lokacin ka ga ni ganau ne ba jiyau ba, na gani kuma na ji, na tuna an yi guje-guje lokacin ana cewa ga ‘yan Tatsine sun zo, ga ‘yan tauri sun zo daga Tudun Wada har menen, an yi ta kashe-kashe. Nan zuwa Bauchi, zuwa su Maiduguri duk abubuwan nan sun faru, su Bulunkutu.
Makarantar da na ce maka na yi a Kagoro, ina gaya maka zuwan da na yi Kagoron nan abin mamaki ne, ina Kagoro na ce, mu ne dalibai da suka yi bakwai na karshe, na yi watanni takwas ne da kwananki 11, to abin mamaki sai rikicin Kafancan, rikicin Kafancan na addini ne, domin wani ne ya shiga addinin Kirista ya fita daga Addinin Musulunci ya shiga Addinin Kirista, ya zo yana magana yana jawabi, sai ya kawo wata ayar ta Alkur’ani bai dauki ayar gaba daya ba sai dauki wani gefe ya fada, shi ne wata mata Musulma Malama ce a makarantar Kwalejin ilimi ta Kafancan, sai ta je ka karbi abin magana sai ta karanto ayar, ta ce a’a ka kawo ayar cikakkiya kada ka kawo wani bangare, don kada ya zama ba su fahimci abin da Kur’ani yake fada ba ko kuma ka fadi abin da kai kake so wa ranka ne.
Aka gama wannan taron ta koma ta ci gaba koyarwarta, sai matasa suka fusata, wai me yasa ta je ta shiga wannan maganar? Shi kenan fa sanadin rikicin, to ka ga ai wannan maganar addini ce. Ka yi maganar Kasuwar Magani ta farko maganar kabilanci ce kuma maganar gona, dole ne mu fuskanci maganar gaskiya mu samu mafita don mu zauna lafiya. Shekarar da na ce maka na gama karatu na samu aiki, shekara bayan wancan rikicin sai ga Zangon Kataf, Katafawa ne da Hausawa suka yi wannan rigimar, amma ya rikide ya zam kamar maganar addini ce, a gaya wa mutane gaskiya a zauna lafiya.
Zamu ci gaba a mako mai zuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!