Connect with us

WASANNI

Magoya Bayan Chelsea Sun Kira Mo Salah Dan Ta’adda

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta fara gudanar da bincike bayan wani hoton bidiyo ya nuna daya daga cikin magoya bayanta na cin zarafin dan wasan baya na Napoli, wato Kalidou Koulibaly a yayin fafatawar da kungiyoyin biyu suka yi a gasar Europa ta ranar Alhamis din data gabata.
Arsenal wadda ta samu nasara da ci 2-0 a karawar, ta fitar da wata sanarwa da ke cewa, ta yi tir da irin wannan cin zarafin na nuna wariyar launin fata, kuma za ta binciko wanda ya aikata haka domin ta hukuntashi.
A bangare guda, shi ma kocin Liberpool, Jurgen Kloop ya yi tir da zagin wariyar jinsi da aka yi wa Mohammed Salah na Masar, kuma ya bukaci haramcin har abada kan magoya bayan Chelsea da suka ci mutuncin Salah.
Wani hoton bidiyo ya nuna mutane shida magoya bayan Chelsea na kiran Salah da mai “kaddamar da hare-haren bama-bamai” wanda kuma cin mutunci ne ga dan wasan da kuma addininsa kamar yadda Klopp ya bayyana.
“Abinda akayiwa Salah bai kamata ba saboda cin mutunci ne ga dan wasan da kungiyar Liberpool da kuma addininsa kuma yakamata Chelsea ta binciko wadanda sukayi laifin domin ta hukuntasu” in ji Klopp
Wannan matalar ta nuna wariyar launin fata na ci gaba da karuwa, domin ko a ‘yan kwanakin nan, sai da aka yi wa ‘yan wasan Ingila a Gasar Neman Tikitin Shiga Gasar Cin Kofin kasashen Turai ta 2020, in da aka yi ta alakanta su da birrai.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!