Connect with us

BIDIYO

Masana’antar Kannywood Da Halayyar Jarumanta

Published

on

A shekarun baya akwai wani babba a cikin ‘yan fim din Hausa da ya yi wata hira da manema labarai kuma a cikin hirar tasa yake bayyana mamakin yadda wasu daga cikin jaruman kannywood musamman ‘yan mata suna fara shiga harkar sai ka ga suna samun kudi suna siyan manya-manyan motoci suna rayuwa mai kyau da jin dadi.
Wannan kuma ba sabon abu ba ne duka wanda yake zaune a jihar Kano ya san halin da ‘yan film suke ciki musamman ‘yan mata wadanda suke kawo kansu cikin harkar daga baya kuma sai su koma wata harkar daban.
Akwai jaruman da sun yi shekara da shekaru suna cikin masana’antar fina-finai amma har yanzu basu ajiye komai a rayuwarsu ba saboda ba ‘yan mata bane.
Yarinya ce za ta baro iyayenta ta tafi kamfanin kannywood cikin lokaci kadan za ka ga yarinya tana hawa manyan-manyan motoci tana saka kaya masu tsada sannan tana kwana a hotel masu tsada.
Sai ni a ganina suna wasu daga cikin ‘yan matan da suke kannywood suna amfani da sunan kannywood ko kuma suna amfani da sana’ar film ne kawai a matsayin hanyar da suke neman kudi a zahirance amma hanyar da suke samun wadannan kudin da ban sana’ar suke samu ba, suna fakewa ne kawai da ita masana’antar fina-finan.
Idan har yarinya kyakkyawa ce fara ko kuma tanada jiki mai kyau tabbas ba za ta dade ba za ta samu abin duniya.
Gaba daya nawa ake samu a film din har da za ka ga yarinya tana hawa motar da Daraktoci da Producers din da suke sakasu a film din ma basa hawa, sannan kuma ba kowacce ‘yar film bace take yi wa kamfani talla da har zata dinga samun karin kudin shiga banda wanda take samu a harkar film din.
Na san yarinyar da ba ta dade da fara harkar fim ba, amma ta fara hawa mota kuma mai tsada, kuma da bakinta take cewa ita fa ba fim ne kawai yake kawo mata kudi ba, to, mene ne sana’arta bayan fim din? Ni dai na san ba ta siyar da komai kuma babu kafin ta samu sana’ar da za ta samu kudin da zai bata damar siyan wannan dankareriyar motar za ta dade.
Kusan shekaru biyu kenan wata yarinya ta yi min waya ta ce daga Kaduna take kuma don Allah tana son in hadata da wani Daraktan wanda zai dinga sakata a fim, sai da muka shafe kusan sati daya muna maganar ina kokarin hanata amma yarinyar nan ta ce ita fa dole sai na kaita idan kuma ban kaita ba za ta nemi wata hanya da kanta, kuma a karshe ban kaita ba kuma ta kai kanta, yanzu tana nan tana hawa motoci a garin Kano, kuma ba a fim kawai ta samu kudin ba.
Saboda haka abin da ya faru tsakanin Hadiza Gabon da Amina Amal ba sabon abu bane a masana’antar ‘kannywood’ kuma duk wanda ya san harkar ya san za su iya abin da ya fi haka.
Akwai wata rana ina cikin wani Hotel a garin Kano na je wajen wani abokina wanda ya yi min waya ya ce in je can in same shi, sai na ga ‘yan fim da yawa suna zaune suna hira, sai aka ce da wata daga cikinsu wai an ga bidiyonta yana yawo a Instagram tana madigo (lesbian) da wata yarinya, kuma yana nan yana yawo a duniya sai ta ce babu ruwanta, wannan ai ba wani abu bane domin ta yi abin da ya fi haka ma a duniya.
Wannan fa ita ce wadda idan ana hira da ita a gidan rediyo take cewa tana yin fim ne domin gyara tarbiyyar al’umma.
Abin da ya faru tsakanin Gabon da Amal tasu ce kawai ta fito fili kuma nan gaba zamu ci gaba da ganin abin da ya fi haka (Allah ya kiyaye)
Yarinya ce fa za ta baro iyayenta daga wata kasar ko kuma wata jihar ta zo wani garin wai fim ta tawo, kuma namiji ne zai sauketa, kai ma dai ka san abin da zai faru.
Amma sai dai dole haka zamu hakura mu zauna da su kamar yadda muke rayuwa da ‘yan siyasa.
Mutum ne zai je ya nemo kudi kawai ya bugo fosta ya ce zai tsaya takara kuma babu wanda zai hana shi idan har yana da kudin da zai baiwa masu zabe kuma zai iya samun nasarar zaben.
Haka su ma ‘yan fim yarinya ce kawai za ta ci abinci ta koshi ta ce ita harkar fim za ta shiga idan har ta baro gaban iyayenta lafiya to tabbas babu wani dan adam da zai hanata ko kuma ya bata shawarar kada ta yi saboda abin da take so kenan.
Kamar yadda a cikin ‘yan siyasa akwai wanda yake tara ‘yan daba yana basu kayan shaye-shaye da makamai haka a kannywood ma akwai wadanda ba mutanen kirki ba ne a ciki.
Kamar yadda muka yarda cewa a cikin ‘yan siyasa akwai mutanen kirki haka ita ma a kannywood din dole akwai mutanen kirki sai dai kawai ya danganta da wanda ka hadu da shi.
Kuma yana daya daga cikin kuskuren da muka yi mu Hausawa da muka yarda cewa duk dan fim dan iska ne kawai, saboda haka mutanen kirki ba za su shiga ba, hakan ya sa mutanen kirkin suka daina shiga sannan kuma su ma sun yarda cewa ba mutanen kirkin bane, hakan ya sa suke abin da suka ga dama sai dai kamar yadda na fada dole akwai mutanen kirki a ciki wadanda idan ka ji halayensu sai ka yaba musu.
Wata rana na je sayayya a ‘ShopRite’ zan kalli wani fim din Hausa sai na ji wani dan cikin kannywood yana gayawa abokinsa cewa “Wato abokina ka yi missing din zuwa Abuja aikin shooting din wani fim domin babu yarinyar da ban ciba a cikin yaran da muka tafi da su,” wannan fa wai shine yake koyar da tarbiyya.
Wata rana wata ‘yar fim ta zo wucewa sai wani a kusa dani ya ce waccen yarinyar mutuniyar kirki ce an ce bata iskanci a cikin ‘yan fim, sai wani a gefe ya ce wallahi karya ne, babu mutuniyar kirki gaba daya a cikin ‘yan fim, wannan shine kallon da muke musu hakan ya sa mutanen kirkin ba za su shiga ba.
Akwai wata jaruma dana sani wacce take sana’ar fim, ita cewa ta yi gaba daya namiji baya bata sha’awa, saboda haka ta daina bata lokacin ta akan namiji ita yanzu ‘yan uwanta mata sune abokokan harkarta.
Wadannan misalai suna nan da yawa saboda haka ko mu yarda ko kada mu yarda rayuwa da ‘yan fim ta zama dole sai dai idan mutanen gari da gwamnati suka so a samu gyara za a iya samu ta hanyar gyarawa din.
Amma ai abin dariya ne wata daga Gabon ko Kamaru ta zo Kano ko Kaduna ko Katsina ta ce wai zata koyar da tarbiyya da al’adar mutanen garin bayan ita ma iyayenta basaso ta shiga fim din ko kuma aurenta ne ya mutu ta shigo harkar film din. Allah ya kyauta.
Sako daga Abba Ibrahim Gwale
Tuntuba: 08060119869
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!