Connect with us

LABARAI

Matar Aure Ta Kashe Jaririyarta Saboda Yawan Kuka

Published

on

Wata mata ta kashe jaririyarta saboda yawan kuka da damunta, kamar yanda jaridar ‘Ebening Reports’ ta ruwaito.
Ita dai uwar, mai suna Abigail Palmer, da farko, ta yi ikirarin cewar, ta tashi barci ne kawai ta ga yar ta ta mai suna Teri-Rae bata da rai; ta mutu.
Mai gabatar da kara a Kotu kan mutuwar jaririyar, ya zargi mahaifiyar da laifin kisan yar ta ta a kokarin ta na hana ta kuka.
Yunkurin kiran masu agajin gaggawa daga birnin West Midlands na kasar England da abu ya faru bai anfanar ba, ta yanda ko da su ka iso gidan, yarinyar ta riga da ta mutu.
Da farko dai, an dauka cewar ko mahaifiyar ba ta da laifi a mutuwar yarinyar, an dauka ko mutuwar Allah da Annabi ce, to amman bayan da aka gudanar da gwaji a asibiti, sakamakon binciken ya nuna karyewar kashin jaririyar.
Ita dai uwar, mashayiya ce (yar kokin), gwaje-gwajen kafin haihuwa sun nuna haka, duk da dai likitocin a wancan lokacin sun boye hakan.
Bayan tabbatar da laifin ta, Alkali ya yanke ma ta hukuncin shekara 13 a gidan kaso.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!