Connect with us

SHARHI

Sharhin Shirin Kwana Casa’in Na Gidan Talabijin Na Arewa24

Published

on

Gidan Talabijin na Arewa24 ya yi fice a tsakanin al’ummar Nijeriya, musamman a arewacin kasarnan. Ana ganin ba komai ya haifar musu da wannan farin jini ba, illa irin shirye-shiryen da suke gabatarwa ga masu kallonsu.
Gidan Talabijin din ya wallafa a shafinsa na Intanet cewa; “an kafa tashar Arewa24 a shekara ta 2014 domin cike gagarumin gibin samar da shirye-shirye masu nishadantarwa da tsarin rayuwa a harshen Hausa, wadanda su ke nuna hakikanin rayuwa a Arewacin Nijeriya, da al’adu da kade-kade da fina-finai da fasahar zane da girke-girke da kuma wasanni.” Sun ci gaba da cewa; “a yau, sama da mutane miliyan 80 masu magana da harshen Hausa a fadin Nijeriya da makwabtan kasashe na kallon tashar Arewa24 cikin sa’oi 24 a dukkanin ranekun mako kyauta akan tauraron dan Adam A yanzu haka, ana kallon tashar Arewa24 akan shahararriyar na’urar tauraron dan adam ta DSTb da GOtb masu tsarin biya. Ana iya samun dukkanin jerin shirye-shiryen tashar Arewa24 kyauta akan shafin ‘YouTube’ kai tsaye bayan an nuna su.”
A kan kuma iya samun Arewa24 a manhajojin tashar na zamani, da kafafen sada zumunta da na wayoyin Hannu. Sun bayyana cewa; tashar na yada
manufofin kamfanin wanda ya shafi “Alfahari da al’adu.” Dakin shirye-shirye na tashar Arewa24 ya samar da shirye-shirye na sama da sa’o’i 2,000 duk da harshen Hausa wadanda suka shafi tsarin rayuwa da kuma nishadantarwa da sauran nau’ikan shirye-shirye daban-daban, sannan za ta ci gaba da samar da shirye-shiryenta masu inganci da nishadantarwa domin jin dadin masu kallon tashar.
Arewa24 ya shahara da shirin nan na ‘Dadin Kowa,’ wanda bayan kammala shi ne, gidan talabijin din ya zo da wani sabon salon shirin, wanda suke yiwa take da ‘Dadin Kowa Sabon Salo.’ Sakamakon yadda shirin ke nuna irin rayuwar al’ummarmu ya sanya a kowanne daren ranar Asabar, dimbin al’umma ne ke zuwa gaban talabijin din su domin kallon wannan sabon shirin da su da iyalansu.
Baya ga wannan shirin, akwai shirin da suke daukar hankalin masu kallonsu, wadannan kuwa sun hada da shirin Gari ya waye, Akushi da rufi, Kyautata Rayuwa, tarkon kauna, sai kuma shirin nan da ya shahara a tsakanin matasa masu sha’awar wakokin Hip-pop wato zafafa goma da dai sauran shirye-shiyensu na fina-finai da al’amuran yau da kullum da al’adu.
Ana tsaka da mararin gidan talabijin din, sai kwatsam suka fito da wani sabon shiri wanda suka yiwa take da ‘Kwana Casa’in.’ Wanda gidan Talabijin din ya fara haskawa a ranar Lahadin da ya gabata, wanda a yau ma ake sa ran za su sake haska ci gaban shirin.
Daga cikin ‘yan wasan da suka fito a cikin wannan shirin akwai; Sani Mu’azu, Ado Ahmad Gidan Dabino, Falalu A. Dorayi, A’isha Auwalu da sauran su. Wadanda suka rubuta labarin fim din sune; Zuwairiyyah A. Girei da kuma Nazir Adam Salih. A inda Salisu T. Balarabe ya ba da umarni.
Tsari da salo da zubin da aka dauka na shirin, yana jan hankali mai kallo. Domin labarin fim cike yake da irin rayuwar ‘yan siyasarmu, dan kuma irin rayuwar kunci da wahala da talaka ke ciki. Shirin fim din ya nuna yadda asibitocin garin ALFAWA ke fama da karancin kayayyakin kula da lafiya. A yayin da wadansu asibitin ke fuskantar matsalar jami’an lafiyar ganin yadda suke tafka cin hanci da rashawa da nuna rashin tausayi. Sannan ya nuna yadda ake hada tuggu da makirci irin na ‘yan siyasa. Shirin bai manta ba da yadda cuta da cin hanci da rashawa ya yi katutu a bangaren jami’an tsaron ‘yan sanda ba, da kuma gurbatacewar tarbiyya da ta ke yawo a Jami’a. Domin a nan an bayyana yadda Fa’iza ta samu karancin tarbiyya tun daga gidansu kafin ma zuwanta jami’ar.
Ni dai da na fara kallon shirin yanayi da dabi’ar da Fa’iza ta fito da shi, har ta fara ba ni haushi, saboda wulakanta direba dinta da ta yi da iyayenta ya bata min rai sosai. Sai dai kuma yarinyarnan ta gidan Gwamna mai tafiya kamar wata kwaguwa wacce Hajiya Hadamammiya (ba sunanta ba ke nan) ta dauko ta daga kauye, ‘yar akwai iyayin tsiya.
A shirin farko da suka nuna; an nuna shaharar wani da ake ce ma ‘MALAM’ wanda yake neman shugabancin garin Alfawa. A yayin da zai kara da gwamna mai ci wanda yake neman zarcewa a karo na biyu. Ko ya ya za ta kaya? Tuni kowannensu ya zare takobinsa domin kaiwa ga gaci. A yayin da Hajiya matar Gwamna ta fi nuna kwadayinta da kumajin ganin mijinta ya zarce a karo na biyu. Ita kuma matar MALAM ganin me ya kai Malam shiga irin wannan gurbatacciyar siyasar? Wani abu dangane da wannan Hajiyar, yadda take da cin tsiya da hadama za ka dauka daga kauyen Handamau aka auro ta. Domin irin hadamar da take yi kamar ta kwana dubu ba ta ci ba.
Shirin mata Iyayen giji kuwa na gidan Talabijin na Alfawa, ya gamu da tasku domin kuwa ya tabo bukatun ‘yan siyasa, kuma tuni suka sanya Manajan gidan Talabijin din ya dakatar da mai gabatar da shirin daga sanya shirin. Wanda Manajan ya yi ruwa ya yi tsaki wajen cikawa ‘yan siyasar burinsu ta hanyar yiwa ‘yar jaridar barazana rasa aikinta. Ko me zai faru da ‘yar jaridarnan bayan ‘yan siyasa sun tura dan daba ya kwace na’urar komfutar ta? Gudun ka da ta saki bidiyon ta wani wuri daban tunda ba a sanya shirin a gidan Talabijin na Alfawa ba? Wannan da ma sauran amsoshi da shirin yake da niyyar amsawa ‘yan kallo za a zuba ido a gani.
A bangaren hoto da murya, dole a jinjinawa gidan Talabijin din, domin sun yi kokarin samar da murya rangadau da hoto tangaran domin masu kallonsu da kuma inganta aikinsu ya kasance a zamanance. Tsari da zubi da salo na shirin, ba shi da bambanci da abubuwan da ke faruwa a kasarnan. Ina ga saboda wannan dalilin ne ma da sauran dalilai ya sanya tun farko shirin gidan Talabijin din ya rubuta cewa; kagaggen labari ne, idan ka ga hali ko yanayi ya zo daya, to arashi ne.
Amma yana da kyau masu tace hoton fim din su lura da kura-kuran da suke yi. Domin sun tafka kura-kuran hada hotuna a wadansu ‘scenes’ din a shirin. Su kara sanya ido sosai ta yadda ba za a rika maimaita kuskuren tace hotunan ba domin aikin su ya inganta ya kuma kaucewa korafe-korafe da yawa.
Muna fatan wannan shiri zai ilmantar da masu kallo, tare da nishadantar da su da kuma fadakar da su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!