Connect with us

LABARAI

Shirin ‘Mafita’ Ta Tallafa Wa Masu Sana’oi A Kano

Published

on

An yaba wa shirin Mafita bisa kokarinta wajen dafa wa ayyukan da take gudanarwa a cikin al’umma musammamn wajen koyar da sana’oi na dogaro dakai dake taimaka wa samar da ayyukan yi, Kwamishinan ma’aikatar tsare-tsare da kasafi na jihar Kano, Alhaji Shehu Na’Allah Kura ya yi wanna yabo a wurin raba kayan sana’oi da Shirin Mafita ta yi ga kungiyoyin masu sana’oi a jihar Kano a harabar ofishinta rabar juma’a.
Ya ce, shirin na Mafita na taimakawa nauyin da ya rataya ga Gwamnati na samar da ayyukan yi ga al’umma, musamman sana’oi na dogaro da kai, duba da hakan Gwamnatin Kano za ta yi kokari wajen sanya hannu dan doreawar ta inganta shi da cigaban tafoyar da shi.
Alhaji Shehu Na’Allah ya kuma yaba wa masu sana’oi da suke aikin sadaukarwa tare da Mafita wajen koyar da sana’oi a fannoni daban-daban a karkashin shirin na mafita da take samun tallafin DFID.
A Jawabinsa shugaban shirin na Mafita Dakta Muhammad Sagagi ya ce, shirin yana gudana ne bisa tallafawar hukumar DFID wanda kuma za su karkare tallafin da suke bayarwa a karshen shekara ta 2020 dan haka ya yi kira ga Gwamnatin jihar Kano a kan ta shigo ta dafa domin a sami ci gaba da dorewar shirin ta gina dangantaka a tsakaninsu.
A jawabinsa na karin haske kan shirin manajan horaswa na shirin na Mafita Alhaji Abba Isyaku Adamu ya ce, sun soma da da horas da sana’oi ga dalibai 2000, yanzu haka akwai dalibai 5000 da za a horas kan sana’oi da suka hada da masu bukatu na musamman. A 2017 an raba wa masu koyarda sana’oi kayan sana’oi haka ma a 2018 an raba musu,wannan karon ma a 2019 za a raba musu bisa tallafawar DFID.
Alhaji Abba ya ce, yanzu haka suna sake duban yara 10,000 wanda an ma tantancesu dan haka suna fata Gwamnatin Kano za ta shigo ta ci gaba da tallafa wa a tsarin na Mafita don fadada ayyukanta zuwa dukkan kananan hukumomin Kano da a halin yanzu sun takaita ne a kananan hukumomi Takwas dake kwaryar birni.
Kungiyoyin sana’oi da suka hada dana Kanikawa da Teloli da masu gini da masu aikin fata da magina da masu gyaran wuta da masu sabya tauraron dan’adan da masu gyaran wayar tafida-gidanka sune suka anfana da tallafin kayan sana’oin da suka hada da kekunan dinki, Injin kwaba kankare kayan gyaran wuta dana wayar tafida-gidanaka da abin kasha gobara da sauran dinbin kaya ga masu horasda sana’oi a shirin na Mafita.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!