Connect with us

RIGAR 'YANCI

Alakar Da Ke Tsakanina Da ’Yan Sara-Suka – Kauran Bauchi

Published

on

Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, ya shaida cewar akwai kyakkyawar alaka mai karfin gaske a tsakaninsa da matasa ‘yan sara-suka, yana mai shaida cewar matasan nan, daga kannensu sai jikokinsu don haka ne ya shaida cewar gwamnatinsa za ta tabbatar da daurasu a kan turbar daidai ba tare da nuna musu kyama ko kadan ba.
Sanata Bala wanda shine zababben gwamnan jihar Bauchi, ya shaida hakan ne a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida jimkadan bayan da ya gana da Lauyoyi 50 da suka dauka wa kansu cewar za su kareshi a kotu kan karar da gwamnan jihar Bauchi da APC suka jigar da su kan zaben gwamnan jihar, yana mai karawa da cewa, gwamnatocin baya sune suka haifar da ‘yan sara-suka kana suka kuma kyamacesu wanda a cewarsa hakan ba daidai bane, ya shaida cewar jawo matasan jika da daurasu a hanya shine kawai zai kawo karshen matsalar sara-suka a jihar.
Sanata Bala ya shaida cewar matsalar ta shafi kowa a jihar, don haka ne ya shaida cewar gwamnatinsa ta zo da tsare-tsaren da suka dace na dawo da matasa ‘yan sara da suka zuwa turbar taimaka wa jama’a a maimakon ganinsu kamar marasa aikin yi, ya kuma shaida cewar duk matashin da ya bijire wa tsarinsu lallai za su dandana masa har sai ya dawo saiti.
A cewar shi; “Wadannan yaran dai ‘ya’yanmu ne, jikokinmu ne. mu yanzu ne muke shiga gwamnati, kuma gwamnatocin da aka yi a baya da gwamnonin da aka yi a baya sune suka haifo sara-suka, sune suka sanya matasan suka zama masu gadin fostoci (Allunan tallah),” A cewar shi.
Ya nuna cewar matsalar ta samu asali ne daga rashin kula da jihar gaba daya, “Yau a Bauchi akwai yara miliyan daya da dubu dari uku 1.3m da basu zuwa makaranta, sune suke zama ‘yan sara-suka. Yau a Bauchi makarantu da dama sun lalace wasu ma a yaye suke, a cikin ajiya daya za ka samu yara 200 babu ma inda yaro zai zauna,” Inji Sanata Bala.
Gwamnan da ke jiran rantsuwar ya daura da cewa gwamnatocin da aka yi a baya a jihar ne suka kawo sara-suka kuma suka wofintar da su wanda a cewarsa shi ba zai yi wannan kuskuren ba; “A takaice dai sune suka kawo sara-suka. Amma mu matasan nan ‘ya’yanmu ne da jikokinmu kamar yadda na fada muku a farko, kuma matsalolinmu, idan su gwamnatocin da suka gabata suna kyamatarsu mu ba mu kyamatarsu,” A cewar shi.
Sanata Bala ya shaida cewar yana da kudurori masu tulin yawa da yake son zuwa da su da zai kai ga saita matasan da suke sara-suka akan turbar daidai, yana mai karawa da cewa a shirye yake ya zage damtse wajen gyara tarbiyya da rayuwar matasanmu, “Muna da wani kuduri da za mu tantance matasan nan, mu gano su waye suke cikin hankalinsu wadanda za su yi mana aiki kamar na duba gari, malaman gona, da sauran aikace-aikacen da za mu samar musu.
“Sannan, za kuma mu duba su waye za mu koyar musu sana’ar hanu wadanda za su zama masu amfani wa kawukansu, iyayensu da kuma al’umma; idan muka yi hakan na san ba za mu rasa wadanda za su bangare ba, da zai zama basu da yawa su ma za mu samar musu da magani. Amma mu a gwamnatance ba mu kyamatar kowa, da matashi da wanda ba matashi ba, da mata da kowa dole ne mu kawo kudirin da zai kawo sauki da gyara wa jama’anmu,” A cewar shi.
Zababben gwamnan da ke jiran rantsuwa a ranar 29 ga watan Mayu, ya kara da cewa sun ga yadda gwamnatin Dankwanbo ta bi wajen magance matsalar ‘yan sara-suka a jihar Gombe, “Kuma wannan maganar da ake yi na sara-suka, an yi sara-suka a Gombe, an ga abun da Dankwanbo ya yi, ya yi abun da nake fadin zan yi, yanzu Gombe babu sara-suka.
Ya kuma ce wadanda suka watsar da matasan nan sai Allah ya tuhumesu; “Su wadanda suka kawo sara-suka suke kyamatarsu sune suka jiyo ga su ga Allah,” A cewar shi.
Daga bisani Sanata Bala ya sha alwashin cewar kamar yadda ake ganin matasa ‘yan sara-suka basu da amfani a cikin al’umma zai tabbatar da dawo da su masu amfani, yana mai karawa da cewa za su bankado su binciko ma’aikatan bogi da ake ce akwai su a jihar Bauchi, inda ya ce za su kakkabe wannan babin hadi da yin sauyin baragurbin ma’aikatan bogi ga matasan da suke zaune babu aikin yi domin komai ya tafi daidai.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!