Connect with us

LABARAI

Al’ummar Sudan Ne Za Su Nada Firaministan Da Suke So, Inji Laftanar Janar Yaseer

Published

on

Sabuwar gwamnatin mulkin sojin kasar Sudan ta bukaci bangarorin siyasa da kuma masu tarzoma da su zabi mutum kamili da za a nada a matsayin Firaministan kasar. Laftanar Janar Yasser Al-Ata, daya daga cikin membobi a majalisar koli ta mulkin sojin, shi ne ya bayyana hakan a lokacin wata ganawa da aka yi tsakanin sojojin da kuma ‘yan siyasa a jiya Lahadi.

Yanzu haka sabon shugaban majalisar koli ta mulkin sojin na ci gaba da daukar matakai da suka hada da tube shugaban Hukumar Leken Asirin kasar da kuma tube jakadan kasar da ke Amurka. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jama’ar kasar ke ci gaba da zanga-zanga dominn ganin cewa, sojojin sun mika mulki ga fararen hula bayan hambarar da gwamnatin shugaba Omar al-Bashir.

Hakazalika masu zanga-zangar sun bukaci a gaggauta gurfanar da al-Bashir wanda ya kwashe shekaru 30 bisa karagar mulkin kasar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!