Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Gurfanar Da Basarake A Edo Bisa Yi Wa ’Yarsa Fyade

Published

on

An garfanar da Goddey Jatto a gaban kotun Benin cikin Jihar Edo, bisa zargin sa da yi wa ‘yar shekara 12 fyade. Shi dai Mista Jatto dan shekara 34 basarake ne, wanda yake zaune a rukunin gidajen ‘Oregbeni Kuarters’ da ke garin Benin.
An bayyana wa kotu cewa, shi wanda ake tuhuma ya tilasta wa ‘yar karamar yarinya zuwa daji, sannan ya yi mata fyade a cikin watan Junairun wannan shekara.
Yarinyar ta bayyana yadda lamarin ya auku. “Lokacin da na ke jiran mahaifiyata a shago, na yanke shawara da in tafi wurin makwabcinmu domin ya taimake ni ya kira min mahaifiyata a wayar salula. “Kafin in isa gidan makwabcinmu, na canza ra’ayina inda na koma baya domin kar in bata wa mahaifiyata rai. Ina cikin tafiya zan koma shago, sai Jatto ya kira ni a kan in taimake shi in kai wa matarsa wasu takardu, na ki zuwa domin ban son mahaifiyata ta zo shago ba ta same ni ba.
“Ya nace min, na zo wucewa kusa da shi sai ya rike min hannu tare da rufe min baki da dayan hannunsa, inda ya kai ni bayan gidansa wurin da ake kamun kifi. “Ya cire min dan kanfai, inda ya fitar da al’auransa waje, sannan ya saka a cikin gabana.
“Abun ya dame ni lokacin da ya gama, ya ba ni naira 200, ya juya min baya yana kokarin yi ta baya. Na dauki dan kanfaina a kasa, inda na ruga a guje,” in ji ta.
Yarinyar ta bayyana cewa, nan take ta bayyana wa mahaifiyarta abin da ya faru.
“Mahaifiyata ta yi kuka sosai har sai da ta ta fadi kasa ta kasa tafiya. Ta sanar wa ‘yan sanda faruwar lamarin, inda muka je ofishin ‘yan sanda a washagarin ranar,” in ji yarinyar lokacin da take yi wa kotu bayanin lamarin.
Mahaifiyar yarinyar ta bayyana wa kotu cewa, lokacin da aka kawo wanda ake tuhuma zuwa ofishin ‘yan sanda, ‘yan sanda sun binciki lamarin, inda suka bukaci in amince a sasanta lamarin tare da wanda ake tuhuma cikin ruwan sanyi, amma na ki amincewa da hakan. Daga baya ta tuntubi jami’an ma’aikatan kula da harkokin mata na Jihar, inda suka tabbatar mata da cewa za su shigar da kara kotu a kan lamarin. Gwamnatin Jihar tana kokarin kare hakkin yara, in ji jami’an ma’aikatan kula da harkokin mata suke fada wa mahaifiyar yarinyar.
Lauya mai gabatar da kara ya kalubanci belin wanda ake tuhuma, inda ya bayyana cewa yana so ya dauke hankali da kuma watsi da shari’an ne.
An dage sauraran wannan kara har sai ranar biyu ga watan Mayu, domin sake sauraron shari’ar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!