Connect with us

RAHOTANNI

An Kama ’Yan Sanda Biyar Bisa Kisan Wata Mata A Legas

Published

on

Rundunar ‘Yan sanda ta Jihar Legas, tana tsare da wasu jami’an ‘yan sanda biyar, wadanda take zargi da harbe wata mata mai shekaru 20, Ada Ifenyi, a Ajegunle, Legas, a ranar Asabar.
Kakakin rundunar, DSP Bala Elkana, ya ce, a cikin wata sanarwa, abin ya faru ne a gida mai lamba 4b, Amusa Lane, daura da titin Ojo, Ajegunle.
‘Yan sandan kuma ana zargin su da harbin wani mai suna, Emmanuel Akomafuwa, 32, da ke gida mai lamba 52, titin Babatunde, Olodi Apapa, a kan layin Akpiri, Olodi Apapa.
“An hanzarta kai wadanda aka harba din Asibiti inda aka tabbatar da mutuwar Ada Ifenyi, shi kuma Emmanuel Akomafuwa, a yanzun haka yana karban magani a kan raunin da ya samua sakamakon harbin da aka yi ma shi.
“Tawagar ‘yan sanda da suke cikin wadanda ake zargi da yin harbin sun fito ne daga ofishin ‘yan sanda na, Trinity Police Station, a yanzun haka kuma suna fuskantar hukunci na cikin gida daga shalkwatar ‘yan sandan da ke Ikeja.
“Tuni ma har an karbe bindigogin da suke a hannun su domin gudanar da bincike. In har an same su da laifi za hukunra su a kotu a bisa laifin kisan kai.
“’Yan sandan da aka kama su ne, Insifekta Adamu Usman, Sajan Adeyeye Adeoye, Kashim Tijani, Lucky Akigbe da Paul Adeoye, sa’ilin da Insifekta Dania Ojo, ya tsere.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kara da cewa, a wata guda kadai da ya gabata, rundunar ta kori jami’an ‘yan sanda hudu a kan yin amfani da ikon da ke hannun su ba bisa ka’ida ba da kuma aikata wasu laifuka da suka sabawa ka’idan aikin ‘yan sanda, an kuma hukunta wasu 41 kamar yanda sakamkon laifukan na su ya nuna.
“An gurfanar da ‘Yan sandan hudu a gaban kotu, kotu kuma ta tsare su a gidan yari,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!