Connect with us

KASUWANCI

An Samu Raguwar Yin Fashi A Akan Tekunan Nijeriya – Rahoto

Published

on

A bisa bayanan kwana-kwanan nan da aka samo daga Cibiyar Kasuwanci ta kasa da kasa (ICC) da kuma daga mahukuntan kula da da tekuna ta kasa da kasa (IMB) sun bayyana cewar an samu raguwar masu yin fashin jiragen ruwa dake dauke da mai da dangogin sa a tekunan Nijeriya a farkon zango na shekarar 2019.
Rahoton na mahukuntan IMB da jairdar Guardian ta samu a ranar Asabar data gabata ya nuna cewar, an samu rahoto yin fashi a tekuna guda 14 a zango na daya idan aka kwatanta da 22 da akayi a a shekarar 2018.
Har ila yau, rahoton na mahukuntan IMB ya nuna cewar, an samu kazantar aukuwa yin fashi akan tekuna a shekarun baya da suka gabata, inda hakan ya janyo sojin ruwa suka kara mayar da habkaili wajen dakile harkarlar ta hanyar yawan yin fatirol akan tekunan da jiragen ruwan su.
Cibiyar dake tara bayanan yin fasakaurin akan tekunan ta IMB ta bayyana cewar, anyo jigilar jiragen ruwa guda 27 inda yan fashin na teku sukayi yunkurin kai masu hari a zango na daya na shekarar 2019 amma basu samu cimma nasara ba.
Darakta a IMB Mista Pottengal Mukundan ya yi nuni da cewar, wannan rahon yana kara bayar da kwarin gwaiwa akan nasarra da aka samu na rage yawan yin fashin a akan tekunan Nijeriya, inda kuma ake sa ran nasarar zata kara dara hakan a shekara mai zuwa.
Mahukuntan na IMB sun kuma tabbatar da mahimmancin musayar bayanai da yin hadaka a tsakain hukumi a fannin don dakile ayyukan masu yin fashin akan tekunan kasar nan.
Mista Pottengal Mukundan kara hadin kai da akayi a tsakain Nijeriya da yan sandan kasar Indonesiya ya taimaka wajen gudanar da yin sintiri akan tekunan kasahen biyu.
A karshe Mista Pottengal Mukundan ya ce, an samu raguwar yin fashin a tekuna a daukacin fadin duniya a zango na farko saboda matakan da aka dauka tsaurara.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!