Connect with us

LABARAI

Ba Za Mu Tattauna Da ‘Yan Bindigar Zamfara Ba – ‘Yan Sanda

Published

on

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Mista Celestine Okoye ya bayyana cewa, rundunar su ba za ta taba tebirin sulhu da barayin da suka addabi jihar Zamfara ba, ba rundunar ‘yan sandan ba kadai, dukkan sauran jami’an tsaron ma.

Jami’in ya bayyana haka ne a garin Talatar Mafara, jim kadan bayan kammala taron shugabannin tsaron jihar Zamfara da aka gudanar jiya Lahadi.

‘In kaji ana maganar sulhu, abun bai yi kamari ba kenan, amma wannan lamarin ya wuce hankali, don haka mun kulle duk wata kofa ta sulhu tsakanin hukumomin tsaro da barayin.’ inji Okoye

Okoye ya kara da cewa nan gaba kadan al’amarin zai zama tarihi, ba lallai mu fadi irin matakan da zamu dauka ba, amma fa za a sha mamaki yadda zamu dau matakin kawo karshen al’amarin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!