Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Taya Firaministan Isra’ila Murnar Lashe Zabe

Published

on

Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya taya takwararsa na Isra’ila wato Firaminista Benjamin Netanyahu murnar sake lashe zaben da aka gudanar a kasar Isra’ila. Netanyahu zai ci gaba da zama Firaministar Isra’ila din ne bayan da jam’iyyar su ta gamayya ta yi nasarar lashe zaben da aka gudanar.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban kasa Buhari, wato Malam Garba Shehu ya sanyawa hannu ya yi fatan alheri ga daukacin al’ummar kasar ta Isra’ila, bayan samun gagarumar nasarar kammala zaben. Inda ya yi musu fatan alheri.

Shugaba Buhari ya ce; yana fatan ci gaba da aiki kafada da kafada da Shugaban Isra’ila  din domin karfafa dankon zumuncin da ke tsakanin Nijeriya da Isra’ila.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!