Connect with us

LABARAI

Dalilan Da Zai Hana Mu Cire Tallafin  Man Fetur A Yanzu- Ministar Kudi

Published

on

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karyata jita jitar da ake yadawa na cewa za a janye tallafin man fetur baki daya. Ministar Kudi, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a jiya Lahadi ta karyata wannan jita-jitar a lokacin da take yiwa tawagar Nijeriya bayanin sakamakon da ya biyo bayan ganawar ta da masu zuba hannun jari da kuma shugabannin Bankin Bada Lamuni ta Duniya wato IMF da kuma Bankin Duniya. Taron wanda ya gudana a Birnin Washington DC na kasar Amurka.

Zainab ta yi wannan furuci ne a matsayin martani da Bankin IMF da ya shawarci Nijeriya cewa idan kasar na so ta tsira da mutuncin ta, to sai ta cire tallafin man fetur baki daya. Wannan furuci ne ya sa masu motoci da sauran ababen hawa suka shiga rudun bin layin sayen man fetur don gudun ka da a kara farashi a lokaci daya.

Rahotanni sun nuna yadda masu gidajen mai suka rika kulle wadansu gidajen man fetur din na su. Sai dai kamfanin NNPC ya yi shelar cewa akwai wadataccen mai a kasa, a daina rige-rigen hada cunkoson sayen mai din.

Ministar da kudi; “Babu wani shiri a nan kusa ko a nan gaba da gwamnatin tarayya ke yi da nufin janye tallafin man fetur.  Jami’an IMF sun ce min zai fi Nijeriya alfanu idan ta janye tallafin man fetur, sai ta yi wa jama’a aiki da kudaden.” .” Inji Minista Zainab.

Ta tabbatar da cewa; a zahirin gaskiya shawara ce mai kyau IMF din ta bayarwa. To amma a Nijeriya ba ta da wani shiri na janye tallafin man fetur. Ta ce; ba a tsara matakan da suka wajaba a janye tallafin ba, idan ma har janyewar za a yi, ta yadda za a fito da hanyoyin saukakawa ga jama’a idan an janye din. Ta tabbatar da cewa; a yanzu dai babu wani shiri na janye tallafin man fetur din. Idan ma har za a cire tallafin, ta ce; to tilas sai mun rika zama da bangarorin da ke da ruwa da tsaki domin samo madadin hanyar saukaka wa jama’a idan har sai an cire tallafin.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!