Connect with us

KASUWANCI

Danyen Man Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Karu Zuwa Ganga Miliyan 1.73 A Watan Maris

Published

on

Danyen man da ake sarrafa a Nijeriya ya karu a cikin watan Maris zuwa ganguna miliyan 1.73 a kullum (bpd) duk da kokarin da gungiyar kasashe masu hakara mai OPEC ta rage yawan danyen man a daukacin fadin duniya don rage yawan farashin na danyen man.
Kungiyar ta OPEC ce ta bayyana hakan a cikin rahoton ta na kwanan, inda rahoton ya ce, Nijeriya a matsayin ta na daya daga cikin yayan kungiyar ta sarrafa danyen n bpd daga 11,000 zuwa miliyan 1.73 a cikin watan Maris na shekara2019 da kuima kara sarafa danyen man na bpd zuwa miliayn 1.7 a cikin watan Fabirairu.
Acewar rahoton, tun daga shekarar 2018 da kuma a cikin zango na biyu na shekarar 2019, Nijeriya ta sarrafa danyen mai da ya kai kimanin bpd miliyan 1.7 idan aka kwatanta da bpd miliyan 1.6 a shekarar 2016.
Rahoton ya kara da cewar, yadda kungiyar OPEC take fitar da danyen man, ya ragu zuwa bpd miliyan 534,000 a cikin watan Maris zuwa bpd miliyan 30.02, inda rahoton ya kara da cewar, yana godiya ga kasashen Saudiyya da Irak akan rage yawan sarrafa danyen mansu da kuma yadda aka kara samun raguwar sarrafa danyen man da kasar Benezuela abode takunkumin da aka kakaba mata na rabar da danyen man.
Wannan shine mafi karanci tun a cikin watan Fabirairun shekarar 2015 a lokacin da suka tura danyen mai zuwa bpd miliyan 29.97.
Fiye da sauran kasahe, Afirka iata ce babba wajen sarrafa danyen mai da suke bukatar farashin na danyen mai ya yi tashin gwaron zabo wanda wannan shine mafi muni, inda kuma ya daidaita akan farashi dala 60 da aka sanya a cikin kasafin kudi na Nijeriya na shekarar 2019.
Masu fashin baki a fannin danyen mai sun bayyana cewar, don a cimma nasarar hakan, Nijeriya tana bukatar kaucewa dakatar da sarrafa danyen manta da kuma fatan sauran kasahsne dake a cikin kungiyarta OPEC don cimma burin hakan duk da cewar, kasashe da dama har yanzu basu bi umarnin da OPEC ta baiwa kasashen masu arzikin danyen mai na rage yawan hakar dayne man da suke hakowa harda Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!