Connect with us

LABARAI

El-Rufa’i Ya Nada Sabon Kwamishinan Kudi Da Babban Akawu

Published

on

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya nada sabon Kwamishinan kudi da alkalin alkalan jihar.  El-Rufa’i ya nada Alhaji Bashir Saidu a matsayin sabon kwamishinan ma’aikatar kudi ta jihar Kaduna. Saidu, shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Kaduna, zai maye gurbin Suleiman Kwari, mutumin da aka zaba a matsayin sanata a zaben da aka kammala.
A jawabin da mataimakin gwamna El-Rufa’i a bangaren yada labarai, Samuel Aruwan, ya fitar a Kaduna, ya ce aikin da ke gaban sabon kwamishinan shine kawo canje-canje masu amfani da muhimmanci a ma’aikatar kudi da za su taimaka wa gwamnatin Nasir El-Rufa’i wajen warware irin kalubalen da zata iya fuskanta a zango na biyu.
Har ila yau, jawabin ya bayyana cewar an nada Mista Idris Samaila Nyam a matsayin sabon babban akawun jihar, yayin da aka nada Umar Waziri, tsohon babban akawun jihar, a matsayin sabon babban manajan kamfanin harkokin saka hannun jari da kudi na jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa Nyam, kafin nadinsa a matsayin babban akawun, ya kasance babban sakatare a ma’aikatar kudi, mukamin da ake sa ran daya daga cikin manyan darektoci a ma’aikatar zai maye gurbin sa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!