Connect with us

KASUWANCI

FIRS Na Shirin Tara Naira Tiriliyan Shida Daga Harajin Da Ba Na Mai Ba A 2019

Published

on

Hukumar tara haraji ta kasa (FIRS) ta samara da cewar, tana shirin tara harajin nairatiriliyan 4.3 daga harajin mai da kuma tara naira tiriliyan 1.7 ta hanyar harajin BAT don zubawa a cikin kasafin kudi na shekarar 2019,
A bisa fashin bakin da akayi akan kundin ya nuna cewar, ana son tara naira tiriliayn 1.7 da za’a karbo daga gun kamfanoni, inda kuma a fannin gas da kudin fito ake sa ran za’a tara naira biliyan 685.63, 6.27 da kuma naira biliyan 17.64
A cikin kundin wanda yake kunshe da harajin hna gajeren zango na kirdadon tara harajin daga shekarar 2019 zuwa shekarar 2020 da aka mikawa Mjalisar kasa.
Har ila yau, a cikin kundin Shugaban Hukumar ta FIRS Mista Tunde Fowler ya sanar da cewar, za’a tara naira tiriliyan 8.8 ta hanyoyi biyu manya na tara harajin.
Mista Tunde Fowler ya kara da cewa, akwai harajin mai inda za’a tara naira tiriliyan 4.3, inda Hukumar take shirin tarawa gwamnati naira tiriliyan 4.5.
A bisa dogon fashin bakin da akayi akan harajin na mai da za’a tara ya nuna cewar, daukacin naira tiriliyan 4.3 da ake sa ran za’a tara daga harajin mai.
Har ila yau, daga kuma fannin da bai shafi fannin mai, kundin ya nuna cewar, ana son a tara naira tiriliyan 1.7 daga harajin kamfanoni, inda kuma ake son a tara naira biliyan 685.63 da naira biliyan 6.27 dakuma naira biliyan 17.64.
Bugu da kari, ana son kluma a tara naira tiriliyan 1.7 daga harajin BAT da harajin ilimi da ya kai naira biliyan 275.39 da naira biliyan 99.78 da kuma naira biliyan 20.01 daga fannin bayanan fasahar zamani.
Hukumar ta bayyana cewar, harajin da take son ta tara a shekarar 2019 zata yi hakan ne a bisa shirin gwamnatin taraya na son farfado da tattalin arzikin Nijeriya, inda Hukumar ta kara da cewar, don a habaka harajin za’a wanzar da shirye-shirye da dama don taimakwa gwamnatin tarayya.
A cewar hukumar, wasu daga cikins usn hadada, fadada rumbun adana bayanai na haraji yadda zai karade daukacin jihihin kasar nan wajen wanzar da harajin BAT.
Hukumar ta bayyana cewar, zata kuma yi aiki da masu ruwa da tsaki da kara tsaurara dokokin biyan haraji don habaka tattalin arzikin Nijeriya.
Har ila yau, Hukumar ta sanar da cewar, zata samar da dabarun tara haraji ta hanyar yin gangami a daukacin fadin kasar nan, musamman don habaka tattalin arzikin Nijeriya.
A karashe hukumar ta ce, zata kuma samar da shiri don baiwa yan Nijeriya kwarin gwaiwar buyan haraji.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!