Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Gobara Ta Kone Shaguna 35 A Kasuwar Kurmi Da Ke Kano

Published

on

Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta bayyana cewa, gobara ta cinye shaguna 35 a kasuwar Kurmin ‘Yan-nama da ke Jihar Kano. Kakakin hukumar kashe gobarar Saidu Mohammed, shi ya tabbatar da aukuwar lamarin lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Lahadi a garin Kano. Ya bayyana cewa, shagona guda 27 sun kone kurmus, yayin da wutar ta dan kama rabin shaguna guda takwas.
“Mun samu kiran wayar salula da misalin karfe 4.56 na asuba, daga wani mutum mai suna Ado Musa, cewa an samu gobara a cikin kasuwa. “Bayan samun labarin faruwar lamarin, nan take muka aika jami’anmu da motocin kashe gobara wurin da lamarin ya auku da misalin karfe 5.03 na asuba, domin su kashe wutar kar ta shafi wasu shaguna,” in ji shi.
Ya shawarci ‘yan kasuwa su kiyaye amfani da duk wani abu wanda zai iya janyo gobara a wurin kasuwancinsu. Mohammed ya kuma shawarci mazauna Jihar a kan su dunga ijiye kayayyakin kashe gobara a cikin gidajensu, domin ko da wutar ta tashi su fara iya kashe ta da kansu, idan ya kazanta kuma to sai su kira jami’an hukumar kashe gobara. Mohammed ya ce, ana gudanar da binciken su sabbabin wannan gobara
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!