Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Gobarar Tankar Mai Ta Ci Rayukan Mutum 12 A Jihar Gombe

Published

on

Mutum 12 sun rasa rayukansu, yayin da mutum 15 suka samu raunika lokacin da wata tankar mai ta yi hatsari ta kama da wuta a kan gadar Bomala da ke Jihar Gombe ranar Asabar. Gidaje guda biyu, motar daukar ruwa, keken nafef da kuma babura da dama ne suka gone a lokacin wannan hatsari. Hatsarin ya sanya yankin ya yi duhu, domin tankar ta lalata falwayar wutan lantarki a yankin.
Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Mary Malum, ta tabbatar da mutuwar mutum 12 a wannan hatsarin. “Ba zan iya tabbatar da karuwar wadanda suka mutu ba, amma na san cewa mutum 12 sun mutu, yayin da mutum 15 sun samu raunika,” in ji Malum lokacin da take tattauna wa da manema labarai ta wayar salula ranar Asabar.
Jami’an ‘yan sanda, hukumar bayar da agajin gaggawa, hukumar kula da hanya da kuma jami’an hukumar kashe gobara na Jihar Gombe duk sun hallacci wurin, domin a samu yadda aka kashe wutar, amma babu isasshen kayan aiki a kasa.
Wani wanda lamarin ya auku a gaban idanunsa mai suna Adamu Kabo, ya bayyana cewa, “Man da ke cikin tankar ya fara zuba ne tun kafin ta isa kan gadar Bomala. Direban tankar ya yi kokarin kauce wa motar ruwa, keke nafaf da kuma sauran babura a kan gadar, hatsarin ya yi kamari.”
Shi ma wani wanda lamarin ya auku a gaban idanunsa mai suna Hasidu Abdulahi, ya bayyana wa manema labarai cewa, mutanen Jihar Gombe tare da hadin gwiwar ‘yan sanda na yankin Pantami, sun yi kokarin zuba ruwa a tankar hukumar kashe gobara na Jihar Gombe, inda suka samu isassahen ruwan da za su kashe wutar. Hasidu ya ce, “Mun yi kokarin kashe wutar da kasa tun da inda za a samu ruwa yana da nisa. “Mun ga sanda direban tankar yake ta fama da tankar a kan gadar. Kan tankar ya fada cikin kududdufi, yayin da jikin kuma ya fadi a kan gadar sannan ya kone kurmus.”
Wani jami’an hukumar NSCDC mai suna Ibrahim, ya bayyana cewa, hukumar kashe gobara suna fuskantar karancin jami’ai da kuma kayan aikin da zai kashe gobara. “An kai kusan awoyi guda uku ana kokarin kashe wutar. Suna ta kaiwa da komowa. Sun kai kusan mitina 50 kafin su iso wurin.” In ji shi.
‘Yan sanda sun killace dukkan bangarorin hanyar guda biyu, wasu matasa sun yi amfani da fakitin ruwa daga cikin matar ruwan wajen kashe wutar.
A halin yanzu dai, gwamnan Jihar Gombe, Dakta Ibrahim Dankwambo, wanda baya cikin Jihar ranar Asabar lokacin da lamarin ya auku, ya jajantawa wadanda lamarin ya rutsa da su.
Da yake magana a madadin gwamar Jihar, shugaban majalisar Jihar Gombe, Mista Nasiru Nono, gwamnan ya bayyana cewa, “Gwamnatisa ta tamu matuka a kan hatsarin mai da ya auku, ta yi alkawarin daukar nauyin jinyar wadanda lamarin ya rutsa da su a asibiti. A ranar Talata, mun gudar da mahawara a majalisa ta yadda za a samu karin hanyoyi, sakamakon karuwar jama’a.
Shugaban majalisar Jihar ya ziyarci asibitin koyarwa na tarayya da ke Gombe, domin duba wadanda suke amsar magani.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!