Connect with us

LABARAI

Gwamna Bagudu Ya Bukaci ‘Yan Jiharsa Da Su Rika Biyan Kudin Wutar Lantarki

Published

on

Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu a yau Litinin ya shawarci al’ummar jiharsa da su daure su rika biyan rukunin kamfanin wutar lantar ta KEDCO kudin wutar sakamakon amfana da wutar da suke yin a tsawon awanni 24 a duk fadin jihar. Gwamnan wanda ya bukaci hakan a garin Birnin Kebbi a yayin wata ganawa da manema labarai sakamakon korafin da masu amfana da wutar lantarkin suka kai, na cewa; an rage tsawon awanni da wutar ke kaiwa daga awanni 24 zuwa awanni 14.

Ya lurantar da masu korafin cewa; yanzu sashen wutar lantarkin yana hannun ‘yan kasuwa ne. Ya ce; a don haka suna ba da wuta ne gwargwadon biyan kudin wutar da jama’a ke yi. Ya tabbatar da cewa; idan har mutane suka gaza biyan kudaden wutan, to tabbas kamfanin da ke kula da wutar lantarkin ba zai iya ci gaba da ba da wutar kamar yadda ya sab aba.

Bagudu ya kara da cewa; gwamnatin jihar ta kashe Naira Biliyan uku daga shekararb 2016 zuwa 2019 wajen samar da Tiransifoma da kuma samar da wutar lantarkin a jihar.

Ya ce; tare da hadin guiwar KEDCO da TCN, har ya sanya jihar ke samun wutar lantarkin har na tsawon awanni 24. Amma yanzu rashin biyan kudin wutar ne ya sa KEDCO ba za su yi ci gaba da ba da wutar lantarkin har na tsawon wannan awanni ba.

Wakili daga KEDCO din wanda yana cikin wadanda aka yi wannan tattaunawar, Malam Sani Sakaba, ya ce; Kamfamin ya yi kokarin ba da wutar lantarki har ta Naira miliyan 900, amma da kyar suke neman hada naira miliyan 300 daga masu amfana da wutar. Sakaba, ya jinjinawa gwamnatin jihar bisa tallafin wata-wata da suke baiwa kamfanin wutar lantarkin.

Inda a karshe ya shawarci kwastamominsu a jihar da su rika biyan kudin wutar lantarkin domin tabbatar da sun ci gaba da amfana da wutar har na tsawon awanni 24.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!