Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Wa Mutum 155,395 Aikin Ido

Published

on

Hukumar da ke kula da lafiya ta jihar Jigawa wato JPHDA a takaice, ta bayyana cewa; tana wani shiri wanda mutum 155,395 daga karamar hukumar Gumel a jihar za su amfana daga aikin ciwon ido da za su yi. Ciwon idon wanda a turance sunansa  ‘Trachoma’, cuta ce da ka iya makantar da mutum idan ba a dauki mataki ba.

Alhaji Habu Magaji, Manajan JPHDA yankin, shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a yau Litinin a garin Gumel. Inda ya tabbatar da cewa; tuni suka samar da maganin ciwon idon mai suna azithromycin da tetracycline domin dakile yaduwar cutar a karamar hukumar ta Gumel din, da ma makwabta irin su Suletantarkar da Gagarawa.

Magaji ya ci gaba da cewa; ba da jimawa ba za su raba magungunan tun daga kan masu shekara biyar zuwa sama. Ya ce; tuni suka horas da jagororin kiwon lafiya a jihar domin gudanar da wannan aikin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!