Connect with us

KASASHEN WAJE

Iraqi Ta Fara Shari’ar Mayakan ISIS 900 ‘Yan Kasashen Waje

Published

on

Wata kotu ta musamman da ke shari’ar wadanda ake zargi da aikata laifuffukan ta’addanci a Iraqi ta fara shari’ar mayakan ISIS wadanda suka fito daga kasashen waje har su 900 da suka tsere daga Siriya bayan farmakar maboyarsu ta karshe da dakarun sojin Siriya suka yi cikin watan jiya. Tun bayan farmakar maboyar karshe ta mayakan na ISIS a Siriya ne, dakarun SDF da ke samun goyon bayan Amurka a Siriyar suka mika tarin mayakan wanda dukkaninsu ‘yan kasashen ketare, ga mahukuntan Iraki lokacin da su ke kokarin tserewa.

Wata majiya daga kotun wadda ta yi shura wajen yanke hukunci kan laifukan ta’addanci, ta ce za a rarraba zaman shari’ar mayakan su 900 ne zuwa rukuni-rukuni don zartas musu da hukunci.

Iraqi wadda tun tuni ta hukuntan wasu tarin ‘yan kasar da ta samu da hannu a kungiyar ta IS, da kan ta, ta bukaci kasashen duniya su biya ta dala miliyan 2 kan kowanne mayaki daya duk shekara don hukunta shi a kasar, ko kuma ta sake su su koma kasashensu.

A shekarar da ta gabata ta 2018, dai Iraqin ta yankewa mayakan ISIS akalla 125 hukuncin kisa sama da 65 da ta yankewa hukuncin a 2017, duk kuwa da ikirarin kungiyar Amnesty International na cewa an samu raguwar yanke hukuncin kisar a duniya. Mayakan na ISIS 900 da suka fito daga kasashen duniya 52 kari ne akan wasu tarin mayakan na ISIS ‘yan kasashen ketare da yanzu haka ke tare a hannun Iraqin ciki har da Faransawa 12.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!