Connect with us

LABARAI

Madaratul Nuraul Huda Tayi Bukin Saukar Karatun Alkur’ani Karo Na 33

Published

on

A ranar lahadin makon daya gabata ne makarantar madarasatul Nurul Huda samaru zariya ta gudanar da bukin saukar karatun Alkura’ani karo na 33 .
Taran an gudanar dashine a bubban filin makarantar Lemu dake samaru a karamar hukumar Sabon Gari a zariya jihar kaduna.
Wakilinmu ya halacci taron kuma ya ruwaito mana yadda taron ya gudana kamar haka. A wannan karo a kalla dubai 28 ne suka sami karbar shahadar maza guda 8 mata 20.
Bubban bako daya albarkaci taron a wannan karo shine, da ga shiek Dahiru Usman Bauchi, Sheik Naziru Usman Bauchi.
Sheik Naziru a jawabinsa ga dalubai a wannan taro ya ja hankalin Dalibaine da su kara kaimi sosai domin karatun addini ba a gamashi kuma yafi komi daraja a rayuwa dan Adam, domin makarancin Alkurani’ani baya tabewa duniya da lahira.
Kuma yace bai kamata aiwa karatun Alkurani’ani rikon sakainar kashi ba. Ya kuma ce a yi karatun boko sosai amma ayi taka tsantsan wajan amfani dashi a dauki abu mai kyau a ajiye abin da ya sabawa Shari’a.
Kuma ya ja hankalin mutane da a kaucewa barace barace kowa ya nemi abin yi dalubi ya zama mai kazanta yace hakan ya saba koyi da Annabi don Annabi bayason kazanta .
Bayan jawabin Sheik din an bayar da tarihin makarantar kamar haka. An kafa makaratarne tun shekarun 1982 ta fara da aji daya rak a shagon gidan Abdulmumini Tanko da malami guda daya rak.
Sheik Umar Ahmed shine tsohon limamin Samaru shine uba ga wannan maksrantar tun farkon kafuwarta. A shekaran1987 ne Alhaji Wada ya safaukar da filin da take a yanzu. A lokacin an gina azuzuwa guda 4 kuma a yanzu makarantar tanada dalubai a kalla guda 2000, wanda a kalla tana bukatar azuzuwa 50.
Nasarorinda da makarantar ta samu sun hada da, bude makarantar boko ta nursery da firamare. Kuma ta samu nasaran samun centre na zana jarabawar JSCE. Kuma a yanzu haka ana koyawa dalubai sana’o’in hannu don magance matsalolin yau da kullun da habaka tattalin arzukin kasa.
Matsalar da makarantar take fuskanta sun hada da, karancin muhalli da rashin zuwan taron PTA da iyaye keyi, sai asusun koyar da sana’o’i da daluban ke gudanarwa na bukatar tallafi don ci gaba da koyar dasu.
An karrama shugan karamar hukumaf Sabon Gari Honorabul Muhammad Usman,da wasu manyan bami anyi taro lafiya an tashi lafiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!