Connect with us

LABARAI

Maganarmu Ta Karshe Da Marigayi Mamman Nasir – Saraki

Published

on

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, ya bayyana bacin ciki game da mutuwar tsohon babban jojin Najeriya, Mai shari’a Mamman Nasir, inda ya tuna lokacin da su ka yi magana ta karshe a rayuwarsa.
Sai kuma ya bayyana Marigayi Nasir a matsayin mashawarcin malami wanda ya ba da gudummawa ga cigaban kasa.
Saraki, a cikin sanarwa da Babban Masanin harkokin Media ya bayar, Yusuph Olaniyonu, a ranar Asabar, ya bayyana cewa, asalin marigayi ya kasance mutumin kirki.
Saraki ya ce, “asali Mamman Nasir dan jarida ne wanda ba shi da tsoro kuma mai aiki wanda ya isa kowane aiki tare da tabbatar da kishin kasa.
“Ya ba da gudunmawar ga ci gaba da shari’a a musamman da kuma al’ummar gabadaya. Dukanmu mun yi rasa shi.
“Ina iya tunawa sosai lokacin da na gabatar da kyautarsa a lokacin bikin baje kolin shekara ta bana, babu wanda zai iya ganin shi a wannan rana kuma ya hango cewa ya na cikin kwanakin karshe, amma Allah ya fi sani,” in ji Saraki.
Saraki ya jajentawa iyalin marigayin da kuma gwamnatin jihar Katsina a kan rashin da a ka yi. Sai ya yi addu’ar Allah ya yi ma sa rahama ya sanya aljanna ce makomarsa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!