Connect with us

KASUWANCI

Masu Fasakaurin Sikari Na Haifar Wa Masana’antun Sikari A Nijeriya Barazana – FMN

Published

on

Mahukuntan kamfanin Fulawa na kasa FMN sun ankarar akan yawan yin fasakaurin Sikari da a ke yi zuwa cikin Nijeriya ta hanyar iyakokin kasar.
Sun yi nuni da cewar, in har ba’a dauki matakan da suka dace ba don magance hakan zai zamarwa da masana’antu dake sarrafa Sikari a cikin kasar nan babbar barazana.
Janar Manja na kamfanin Golden daya daga cikin sashen kamfanin Fulawa na Flour Mills Plc Mista Maniatis Loannis John ne ya sanar dahakan a jihar Legas a lokacin dayake tattaunawa da manema labarai.
Mista Maniatis Loannis John ya yi nun da cewar, yawan fasakaurin Sikari da akeyi zuwa cikin Nijeriya yana shafar ayyukan sarrafa sSikari da kamfanonin a cikin Nijeriya sukeyi, inda ya ce hakan yana kara zamowa kamafnonin na cikin gida tirniki.
A cewar Mista Maniatis Loannis John burin da gwamnatin Nijeriya take dashi na samar da wadataccen Sikari a kasar zaiyi wuya in har gwamnatin bata dauki matakan dakile masu yin fasakaurin Sikari zuwa cikin Nijeriya ba.
Mista Maniatis Loannis John ya kara da cewa ayyukan na yan fasakaurin Sikari zuwa cikin Nijeriya ya dakilewa gwamnatin tarayya burin ta na wanzar da shirin sarrafa Sikari a cikin kasar na (BIP) don habaka tattalin arzikin Nijeriya ta fannin sarrafa Sikari a cikin kasar nan.
Ya bayyana cewar, bayan da kamfanin Flour Mills ya zuba jarin dala biliyan 50 a kamfanin sarrafa Sikari na Sunti Golden Sugar Estate dake a yankin Mokwa cikin jihar Neja, a yanzu hakan kamfanin yana fuskantar barzana saboda ayyukan masu yin fasakaurin Sikari zuwa cikin Nijeriya.
Acewarsa, a na sa ran kamfanin zai sarrafa tan miliyan daya na Sikari a duk shekara, sai dai, ya nuna jin tsoaron sa akan karuwar ayyukan masu yin fasakaurin Sikarin zuwa cikin Nijeriya, inda ya ce, hakan zai shafi kirdadon da akyi na yadda kamafin zai sarrafa Sikari har tan miliayn daya a shekara, musamman iodan gwamnatin tarayya bata dauki babban mataki akan masu yin fasakaurin Sikarin ba.
Ya bayyana cewar, kamfanin na Sunti Golden Sugar Estate dake a yankin Mokwa, yana da kadada data kai kimain 17,000 kuam yana da karfin da zai iya sarrafa Sikari tan 4,500 a kullum.
A cewarsa, kamafin Flour Mill na kasa ana sa ran zai samu daga tan 6,000 zuwa tan and 7,000 a duk shekara daga kamfanin na Sunti Golden Sugar Estate, inda ya ce sai dai, masu yin fasakaurin ne suke hana ruwa gudu saboda ayyukan su na fasakaurin Sikari zuwa cikin Nijeriya.
A karshe Mista Maniatis Loannis John ya ce, “ Muna son mu sarrafa kashio 20 bisa dari na Sikarain da ake bukata a Nijeriya a cikin shekaru shida masu zuwa”.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!