Connect with us

LABARAI

Masu Noman Rani Sun Koka Kan Matsalar Karancin Mai A Kebbi

Published

on

Manoman rani sun soma kokawa a kan matsalar mai da kunno kai a wadansu sassan jihar Kebbi. Wakilinmu ya zagaya wadansu gidajen mai a garin Birnin Kebbi da kuma wadansu sassa idon ganewa idonsa.
Malam Bashar Kabiru Bagaye karamar hukumar mulki ta Augie ya shaidawa wakilinmu da cewa tun da suka soma aikin noman rani a bana suna sayen man fetur a kan naira dari da arba’in da biyar amma sai ga shi kwatsam farashin ya tashi zuwa naira dari da saba’in.
Ya yi kira ga yankasuwa da su ji tsoron Allah su daina tsanantawa ga al’umma.
Malam Shu’aibu, Manajan gidan man Mainasara Katanga da ke garin Argungu a lokacin da wakilinmu ya ziyarci gidan man sa ba ya nan kuma babu fetur sai dai gas sannan kuma ba ya nan wakilinmu ya kira shi ta waya amma dai ya yi alkawarin kira daga baya idan ya kammala abinda ya ke yi amma dai har zuwa lokacin hada wada wannan rahoton bai kira ba.
Alhaji Murtala Suleman Argungu wanda ya ce tun karfe uku na dare ya he gidan mai na gwamnati NNPC da ke kan hanyar Sokoto amma sai kusan large goma na safe ya sami mai.
Ya koka bisa ga yadda yan kasuwar mai ke takurawa al’umma saboda cimma wata bukatar kawnansu wacce ya ce ba cigaba ba ne.
Ya yi kira ga hukumar da abin ya shafa da ta tsawata saboda kada murna ta koma ciki wanda bayan matsalar mai ana ganin ta zama tarihi amma sai ga shi wasansu suna neman dawowa da ita.
Shi kuma Malam Sanusi Umar manajan gidan man NNPC ya bayyanawa wakilinmu da cewa shi bai san da akwai wata matsalar mai ba ballantana abinda ya haddasa ta illa dai kawai ya wayi gari ya ga cikoso a gidan mansa.
Ya dai bayarda tabbacin mai ba zai yanke ba In sha Allahu a wannan gidan mai na NNPC kuma a farashin da a ke sayarwa na #143:00.
Alhaji Garba Kabo Shugaban kamfanin Gande Petroleum kuma Shugaban masu sana’ar mai a karamar hukumar mulki ta Argungu inda a nan ne aka fi nomanrani a yanar gizo ya bayyana wa manema labarai da cewa yana daga cikin dillalan albarkatun man fetur da bayarda gudummawa a wannan yankin saboda kusan shi ne ke samarda kashi biyar daga cikin goma na man fetur amma a halin yanzu duk gidajen man sa ba wanda ke da mai kuma ya kalubalanci duk wanda ke zarginsa da boye mai ko rufe gidajen man sa saboda ya takura wa al’umma saboda mai ya kara kudi ko wata hukumar da a zo a bincika kuma idan aka sami mai ya yarda da a hukumta shi.
Ya ce yanzu haka tun bayan kammala zaben gwamnoni ya tura motoci takwas a Legas amma ba wacce ta sami Lodi kuma bai wsan dalilin haka ba
Hukumomi dai an ce sun zagaya inda suka rufe wadansu gidajen mai a jihohin Sakwkwato, Kebbi da kuma Zamfara.
Jama’a dai suna ta’allaka wannan matsalar ne da masu gidajen mai din dai sun fake ne guzuma domin su harbi karsana saboda a duk shekara ta Allah sukan yi kokarin haddasa wani abu da zai kawo tsadar mai a lokacin aikin noman rani ko kuma karshen shekara saboda samun kazamar riba a sanadiyyar kara farashin man fetur.
Yanzu haka dai farashin mai ya tashi daga naira Dari da arba’in da biyar zuwa zuwa naira dari da sittin a wadansu sassan jihar Kebbi sanadiyyar karancin mai ko kuma rashin sa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!