Connect with us

RAHOTANNI

Matsalar Tsaro: SERAP Ta Nemi Buhari Da Gwamnoni Su Yi Bayanin Kudin Da Su Ke Kashewa

Published

on

Kungiyar nan mai zaman kanta ta kare hakkin dan adam (SERAP), ta aike da wani sako ga shugaba Buhari, inda take neman shugaban da kuma dukkanin gwamnonin kasar nan 36 da su hanzarta bayyana kudaden da suke kashewa daga cikin asusun nan na tsaro tun daga shekarar 2011 zuwa 2019.
Cikin wasikar bukatar hakan da kungiyar ta aike daban-daban ga shugaban kasan da kuma gwamnonin Jihohin, SERAP, ta ce akwai bukatar samun bayanan domin tantance ainihin kudaden da aka kebewa sashen tsaron, da kuma tabbatar da ana kashe su a bisa ka’ida.
Bayanan da ake nema, a cewar kungiyar sun takaita ne a kan bayanan da ake iya ganin su musamman a kan matakan da aka dauka aka kuma aiwatar da su a kan tsaron, amma ba su hada da wadanda ake kashewa a kan samar da bayanan sirri ba.
Ta kuma bukaci a kafa gidauniyar hadin gwiwa a kan fannin na tsaro a tsakanin gwamnatin tarayya da kuma gwamnonin kasar nan 36, wacce za ta kasance da kakkarfan tsari da manufa da kuma bin diddigi na kwarai, wacce za ta maye gurbin asusun tsaro da a kan kebewa gwamnatocin.
Takardar bukatar hakan mai dauke da kwanan watan 12 ga watan Afrilu, 2019, wacce kuma ke da sa hannun mataimakin daraktan kungiyar, Kolawale Oluwadare, kungiyar ta ce, “Sashe na 14(2)(b) na tsarin mulkin Nijeriya 1999 ya tanaji cewa, batun tsaro da jin dadin al’umma shi ya kamata ya zama abu na farko ga dukkan gwamnatoci.
SERAP ta ce, ta damu ne da yanda a maimakon a ce ana yi wa al’umma aiki da kudaden da ake kebewa din domin sha’anin tsaro, sai ya kasance wasu manyan jami’an gwamnati ne kawai suke cin gajiyar su domin biyan bukatun kansu a mataki na tarayya da kuma Jihohi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!