Connect with us

KASUWANCI

Nijeriya Ba Za Ta Cimma Nasara Kan Rarar Danyen Mai – IMF

Published

on

Hukumar bayar da lamuni ta duniya IMF ta sanar da cewar, Nijeriya bazata cimma nasarar da ta ke son cimm ba na rarar danyen manta da take son cimma burin ta ba.
Darakta a Hukumar ta IMF a sashen samar samar da ci gaba a nahiyar Afirka (AFR) Mista Abebe Selassie ne ya sanar da hakan a ranar asabar data gabata a birnin Washington dake cikin kasar Amurka a lokacin taron tattalin arzikin nahiyar Afirka.
Abebe Selassie ya ci gaba da cewa, “ Mun damu matuka akan tattalin arzikin nahiyar Afrika domin in zaku iya tunawa, an kafa ECA yadda zata adana kudi koda farashin danyen mai zai yi tashin gwaron zabo”.
Darakta a Hukumar ta IMF ya kara da cewar, idan farashin danyen mai ya fadi haka tattalin arziki shima zai shiga wani mawuyacin hali, inda ya yi nun da cewar, adana kudade da yawa a ECA a lokacin da farashin na danyen mai ya kai dala 100 zuwa dala 120 na ko wacce ganga daya.
A cewarsa, rashin kokarin da aka samu a ECA ne ya sanya IMF ta dora Nijeriya a a matakin kasar da ta kai ta biyu wajen yin amfani da kudin ajiyarta na kasar waje.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!