Connect with us

WASANNI

Real Madrid Na Dab Da Sayen Sabon Dan Wasan Argentina

Published

on

Rahotanni daga kasar Argentina sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid za ta kammala siyan dan wasa Ezekuel Palacios a wannan satin bayan da kungiyar da dan wasan yake buga wasa, River Plate ta amince da cinikin.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, an kammala duk wata yarjejeniya kuma da zarar dan wasan yadawo daga hutun da kungiyar tabashi sakamakon ciwon dayaji zai kammala komawa Real Madrid domin yafara buga wasa a sabuwar kaka mai zuwa.

Kungiyoyin PSG da Manchester City dai sun nemi dan wasan tsakiyar dan asalin kasar Argentina sai dai Real Madrid tayi saurin kammala cinikin domin kada wadannan kungiyoyi su shiga cinikin.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai an santa da siyan manyan ‘yan wasa a duniya sai dai a ‘yan shekarun nan kungiyar ta canja salon yadda take siyan ‘yan wasa inda yanzu take yawan siyan matasan ‘yan wasa.

Kungiyar dai ta siyi matasan ‘yan wasa kusan guda bakwai daga kakar wasan data gabata zuwa yanzu kuma nan gaba ma kungiyar zataci gaba da siya saboda a cewar shugaban kungiyar, Florentino Perez, siyan matasan ‘yan wasa yana da amfani kuma dasu ake gina kungiya kuma hakanne yasa kungiyar ta siyi dan wasan baya Elder Militao daga FC Porto.

Palacios dai ya buga wasanni 47 sai dai guda ashirin daga ciki a wannan kakar ya bugasu kuma ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin nahiyar kudancin amurka bayan sun doke abokiyar hamayyarsu, Boca Junior.

Real Madrid dai ta ware makudan kudade domin siyan sababbin ‘yan wasa kuma sabon kociyan kungiyar, Zinadine Zidane ya tabbatar da cewa babu dan wasan da zaiyiwa kungiyar tsada indai tana sonsa siya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!