Connect with us

MAKALAR YAU

Rigakafin Garkuwa Da Mutane!

Published

on

A lokuta da dama mutane kan yi korafi kan masu bin hanyar Abuja zuwa Kaduna. Masu irin wannan korafin suna ganin mai za sa a ci gaba da bin hanyar alhali kuma kusan kullum rahotanni marasa dadi ne ke fitowa na garkuwa da mutane. Idan ka kalli korafin da kyau yana da ma’ana, ko ba komi ya bubbugo ne daga kauna, nuna damuwa da takaici.

Sai dai, hanzari ba gudu ba, da yawan wadanda ke bin hanyar nan ta Abuja zuwa Kaduna, mafi yawansu lalura ce ke tilasta musu aikata hakan. Saboda ai babu wanda saboda tsabar ganganci ya san cewa, debe mutane a ke yi a hanyar kamar nunannen Tumatur, amma kuma ya bi cikin shauki don dai kawai a sace shi.

Wani matafiyin uzuri ne da babu yadda zai yi kan shi. Zai yiwu a ce ai akwai jirgin kasa mai zirga-zirga a hanyar. Eh, duk da haka nan, ai ba a kowacce dakika ne za ka iya zuwa tashar jirgin kasa ka samu jirgi mai tafiya ba. Jirgin yana da jadawalin tashi. Idan uzurinka ya saba da jadawalin tashin jirgin sai dai ka yi dayan biyu, ko dai ka hakura da tafiyar ko kuma ka bi mota.

Bisa wannan dalili ne ya sa na kuduri aniyar yin wannan rubutun, ko ba komi za mu tattauna wasu daga cikin abubuwan da suka bayyanar mana dangane da wannan annoba ta garkuwa da mutane.

A shekarun baya, idan ka rantsewa al’ummar arewacin Nijeriya cewa, lokaci zai zo da za a fuskanci ukubar masu garkuwa da mutane, zai yi wahala ka samu wanda zai fahimce ka. Wanda yanzu ga zamani ya kawo mu, ta’asar da muke ta jin duriyarta a kudancin Nijeriya, yau a kofar gidajenmu ta zo, tana barazana ga kowa.

Ya zuwa yanzu, mun iya fahimtar salo da dabarun yadda wadannan mutane suke aikinsu. Mafi bayyana ga gamagarin al’umma shi ne, a sace mutum daga baya su yi amfani da wayar salula wurin kiran makusantansa domin bayyana farashin dan uwansu.

Akwai wasu karin dabaru da salo wanda wadannan mutane ke amfani da su, daga ciki har da wanda mu ne da kashin kanmu muke taimakawa hakarsu har ta cimma ruwa. Hakan kuwa na tattare da tsarin mu’amalarmu ta yau da kullum. Mafi yawa na daga garkuwa da mutane da a ke yi a kauyukan Katsina, Zamfara da Kaduna ana aikata su ne sakamakon rahoton sirri da masu garkuwan suke amfani da shi.

Akwai daga wasu kauyuka da na samu labarin cewa, da zarar bako ya ziyarci gidansu ko na ‘yan uwa, ‘yan rahoto za su sanar da masu garkuwa game da zuwansa. Don haka garkuwa da mutane a wadancan kauyukan ana amfani ne da bayanan sirri.

Hatta tsarin gudanarwar masu garkuwar kan hanyoyin Abuja zuwa Kaduna, da na Zamfara da Katsina duk suna amfani da bayanan sirri. Sai dai a mafi yawan lokuta sun fi amfani da neman sa’a, su tare hanya cikin shirin kan mai uwa da wabi.

Tunda yanzu mun fahimci cewa, mugayen mutanen nan suna amfani da bayanan sirri ne wurin yin garkuwa da mutane. Toh ya rage namu don yi wa mu’amalarmu ta yau da kullum garanbawul, ta yadda ba za mu zama silar sakin bayanan sirrin da za su kai ga yin garkuwa da mu ba.

Misali, mutum ne zai yi tafiya, sai ya hau soshiyal midiya ya fara sanarwa kamar haka, ‘Ina bukatar addu’arku, zan tafi Katsina’. Wannan bayanin kadai ya isa a yi binciken gaggawa kan danginku da ahalinka. Idan a danginku akwai mai hannu da shuni, shi kenan ka zama nama. Sai su yi amfani da wannan su sace ka kawai.

Baya ga dora duk wani motsinmu a kafafen sadarwa na Intanet, akwai kuma yawan surutu. A wannan halin da muka tsinci kawunanmu a ciki na rashin tsaro da fargaba, ya wajaba a kawunanmu na mu yi wa harshenmu linzami. Ba komi ne za mu tattauna da mutane ba, komi kusancinmu da su kuwa. Domin wani ba da gangan ko don ya cutar da kai zai saki wani zancen ba – barin zance ne kawai zai afku.

Muhimmi a nan ma dai, shi ne mu zama masu ajiye sirrukan rayuwarmu, ba komi bane sai kowa ya sani, musamman ma sirrukan da suka shafi kudi da wata karuwa. Domin da wannan ne mamuguntan suke auna kowa, shin ka cancanci a sace ka ko a’a.

Dangane da bin hanyoyin da a ke wannan garkuwa kuwa, musamman hanyar Abuja zuwa Kaduna, na taba sanar da wani abokina cewa, matafiya na bukatar addu’a da kiyayewa. Mu zama masu kiyaye fadin lokutan da za mu kama hanyar fara tafiya. Sannan kuma mu kiyaye lokaci. Babu alheri ga bin hanyar nan da asuba, kamar yadda ta ke cike da hadurra idan a ka bi ta da yammaci zuwa farkon dare. Su kansu masu garkuwa suna amfani da daukewar zirga-zirgar jama’a. Asuba zuwa wayewar gari lokaci ne mai dadin sha’ani gare su. Yayin da farkon yammaci zuwa farkon dare ma ke yi musu daidai. Wadannan lokutan da na lissafo, gabadayansu za a ga cewa gari ya kan yi tsit, babu zirga-zirga kamar yadda a kan samu a farkon ketowar rana, da tsayuwar ranar a tsakiya zuwa farkon faduwarta.

Wannan shawara ce ga al’umma don mu kiyaye, kuma mu hankalta. Domin annobar ta zama abin da ta zama. Sai dai a yi addu’ar Allah Ya kiyaye ya tsare mu daga sharrin masu sharri, Aameen. Mu hadu mako mai zuwa!
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!