Connect with us

LABARAI

Shugaba Buhari Ya Sha Alwashin Kwato Sauran ‘Yan Matan Chibok

Published

on

A daidai lokacin da ake cika shekara 5 da sace ‘yan matan makarantar Sakandiren garin Chibok a jihar Borno mai fama da rikicin Boko Haram, gwamnatin Nijeriya ta ce har yanzu ba ta fitar da rai kan cewa nan gaba kadan za ta kammala ceto ‘yan matan da suka rage hannun Boko Haram ba. Tun a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne, mayakan kungiyar ta Boko Haram suka farwa makarantar Sakandiren ‘yan matan garin Chibok tare da sace dalibai fiye da 200. Yanzu haka dai akwai dalibai fiye da 100 da ke hannun mayakan wanda ake ci gaba da tattaunawa wajen ganin an kammala ceto su.

Gwamnatin Muhammadu Buhari, wanda na cikin alkawuranta na neman zaben shekarar 2015 dawo da ‘yan matan na Chibok, ta ce har yanzu ta na ci gaba da kokarin ganin an kammala kubutar da ‘yan matan. Gwamnatin a ‘yan watanni bayan hawanta mulki ta yi nasarar kubutar da wasu tarin ‘yan matan na Chibok wadanda wasun su aka yi musayarsu da wadansu mayaka na Boko Haram wasu kuma rahotanni ke nuna cewa an biya kudin fansa kafin kubutar da su.

Sanarwar da Malam Garba Shehu mai magana da yawun shugaba Buhari ya fitar a shekaranjiya Asabar, ta ruwaito shugaban Nijeriyar na cewa ba su fidda rai na samun damar kammala kubutar da ‘yan matan na Chibok ba.

Tun a wancan lokaci dai akwai wasu ‘yan mata daga cikin daliban na Chibok da suka zabi ci gaba da zama tare da mayakan na Boko Haram maimakon komawa ga danginsu. Akwai dai wasu bayanai da ke nuna cewa gwamnatin Nijeriyar na tattaunawa da kungiyar ta Boko Haram don ganin an kammala kubutar da ‘yan Matan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!